Iran ta ce duk maƙociyar da ta bari aka yi amfani da ita wurin kai mata hari 'abokiyar gaba' ce

Mahukunta a Tehran sun yi wannan gargaɗi ne bayan shugaban Amurka Trump ya ce ƙasarsa ta tura ayayin jiragen yaƙi a kusa da Iran.

By
Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta tura ayarin jiragen yaƙi a kusa da Iran / Reuters

Iran ta yi gargaɗi cewa duk wata ƙasa da ke maƙotaka da ita da ta bari aka yi amfani da ita wurin kai mata hari za ta ayyana ta a matsayin abokiyar gaba, bayan wani ayayi na jirgin ruwan Amurka mai ɗauke da jiragen sama na yaƙi ya isa tekunan Gabas ta Tsakiya.

Kwamandan Rundunar Zaratan Soji ta Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) ne ya yi wannan gargaɗi ranar Talata a yayin da ake ci gaba da zaman ɗarɗar a yankin.

"Ƙasashen da ke maƙotaka da mu abokanmu ne, amma idan suka bari aka yi amfani da ƙasarsu ko sararin samaniyarsu ko kuma tekunansu wajen kai wa Iran hari, za mu ayyana su a matsayin abokan gaba," in ji Mohammad Akbarzadeh, mataimakin shugaba na dakarun sojin ruwa na IRGC, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Fars news agency ya ruwaito.

Sabon ayarin jiragen yaƙi ya nufi Iran

Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta tura ayarin jiragen yaƙi a kusa da Iran, inda ya bayyana fatan ganin mahukuntan Tehran su amince da yarjejeniya da Washington.

"Yanzu haka sabon ayarin jiragen yaƙi masu kyawu sun nufi Iran," a cewar Trump a yayin wani jawabi ranar Talata.

"Ina fata za su cim ma yarjejeniya."

Trump ya yi wannan kalami ne a yayin da Amurka ke ci ƙara harkokin soji a yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya ƙara tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Washington da Tehran.