| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Mutum 5 sun mutu a hare-haren makamai masu linzami na Houthi a fadar shugaban ƙasar Yemen
Kazalika, a cewar ministan lafiya na ƙasar Yemen mutane 16 sun jikkata a hare-haren makamai masu linzami da mayaƙan Houthi suka kai fadar shugaban ƙasar da ke birnin Aden.
Mutum 5 sun mutu a hare-haren makamai masu linzami na Houthi a fadar shugaban ƙasar Yemen
Dakarun Yemen masu kawo ɗauki na tafiya a gefen bakin teku tsakanin Aden da Mokha, a Yemen ranar 5 ga watan Oktoban 2026.

Aƙalla mutane biyar ne suka mutu, yayin da 16 suka jikkata bayan mayaƙan Houthi sun kai hari da makamai masu linzami a fadar shugaban ƙasar Yemen ta Al-Maashiq da ke birnin Aden, wanda a halin yanzu shi ne cibiyar gwamnatin ƙasar, a cewar Ministan Lafiya na ƙasar.

Wata majiya daga gwamnati ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu a ranar Alhamis cewa, an yi amfani da makamai masu linzami guda biyar wajen kai harin, kuma akwai wasu mambobin gwamnati a cikin fadar a lokacin da lamarin ya faru.


Ministan Lafiya na Yemen, Qassem Buhaibeh, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata sun haɗa da jami’an tsaro da ma’aikata fararen-hula da ke aiki a harabar fadar shugaban ƙasar.


Ya bayyana harin a matsayin “irin wanda aka kai wa gwamnatin Yemen a filin jirgin saman Aden a watan Disambar 2020.”


Sai dai ya jaddada cewa, gwamnatin za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta tare da jama’a.


Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta ƙasar ta ce Firaminista Shaya al-Zindani da sauran mambobin gwamnati suna cikin ƙoshin lafiya bayan harin.

Masu AlakaRikicin Saudiyya da Houthi: Shin zai fadada a Gabas ta Tsakiya? - TRT Afrika - TRT Afrika


A halin da ake ciki, wasu bidiyoyi da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun nuna hayaƙi mai yawa yana tashi daga cikin fadar Al-Maashiq.


Haka kuma kamfanin dillancin labarai na Saba mallakin gwamnatin Yemen ya ruwaito cewa, mayaƙan Houthi sun kai wasu hare-haren makamai masu linzami a wasu unguwanni a birnin Marib.


Tun da farko, kamfanin ya ce ƙungiyar ta yi luguden wuta kan gidajen fararen-hula da ke kusa da fadar shugaban ƙasar.


Gidan talbijin na Al-Masirah da ke ƙarƙashin ikon Houthi shi ma ya ruwaito cewa, wata majiya ta soji da ba a bayyana sunanta ba ta tabbatar da kai harin kan fadar, sai dai ba ta bayar da ƙarin bayani ba.


Wannan shi ne hari na farko da aka kai fadar shugaban ƙasar tun bayan sake ɓarkewar yaƙi tsakanin mayaƙan Houthi da gwamnatin Yemen da ƙasashen duniya suka amince da ita a watan Yuli.


Ƙasar Yemen ta sha fama da rikici tun daga shekarar 2014, lokacin da mayaƙan Houthi suka ƙwace iko da babban birnin ƙasar, Sanaa, lamarin da ya tilasta wa gwamnatin da ƙasashen duniya amincewa da ta bar babban birnin.


A shekarar 2015, wani haɗin gwiwar ƙasashe ƙarƙashin jagorancin Saudiyya ya shiga yaƙin domin tallafa wa gwamnatin Yemen.


Rikicin da ake ciki yanzu ya sake tsananta ne a watan Yuli, bayan rugujewar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma a shekarar 2022.