| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda 25 masu alaƙa da Daesh a jihar Borno
Hukumomin sun ce an kuma lalata ababen zirga-zirga da na jigilar kayayyakin 'yanta'addan.
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda 25 masu alaƙa da Daesh a jihar Borno
Nijeriyta ta ɗaɗe tana fama da hare-haren gungun 'yanbindiga da 'yanta'addan Boko Haram da ISWAP / Reuters
23 Fabrairu 2026

Dakarun Nijeriya sun kashe aƙalla 25 daga cikin ‘yan ƙungiyar ISWAP mai alaƙa Daesh a wani samame da suka kai a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Sani Uba, jami’in watsa labaran runduna ta musamman da ke yankin, ya bayyana ranar Lahadi cewa dakarun sun kai samamen kan ‘yan ISWAP ne a Limankara da Kukawa, kamar yadda wata sanarwa da ya fitar ta bayyana.

“Yayin musayar wutar, an kashe ‘yanta’adda 15 sannan gomman ‘yanta’adda sun tsere da raunuka na harbi,” in ji Uba.

Ya ƙara da cewa na’urar tattara bayanai ta sama ta bi ‘yanta’adda da ke tserewa kan babura biyar, inda wani harin ba tare da kuskure ba “ya kashe ƙarin ‘yanta’adda 10 ".

Ya ƙara da cewa an lalata ababe da yawa na tsaro da na jigila da ‘yanta’addan ke amfani da su.

Masu AlakaTRT Afrika - Nijeriya: 'Yanbindiga sun kashe mutum 50 da garkuwa da wasu da dama a Jihar Zamfara

An kuma ƙwace motoci biyu da makamai da kuma harsasai masu yawa daga hannun ƙungiyar.

Nijeriya ta daɗe tana fama da hare-hare daga ‘yanbindiga da kuma ƙungiyoyin ‘yanta’adda na Boko Haram da ISWAP a sassan ƙasar.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa ana yi wa Kiristoci “kisan gilla” a Nijeriya.

Amma mahukunta a Abuja da yawancin ƙwararru sun ce tashin hankalin da ake yi a Nijeriya na shafar Kiristoci da Musulmai ne ba tare da wariya ba.

Ranar 25 ga watan Disamba, sojin Amurka sun ƙaddamar da hare-haren sama a jihar Sokoton Nijeriya.

Hukumomin Nijeriya daga baya sun bayyana cewa an ɗauki matakin ne tare da saninsu kuma an kai hari ne kan ‘yanta’adda masu alaƙa da Daesh.

An tura wasu sojojin Amurka 100 zuwa Nijeriya a wani ɓangare na ƙarin haɗin kai na soji domin yaƙar ‘yanta’adda. Sai dai kuma Nijeriya ta ce dakarun Amurka ba za su shiga yaƙi ba kai-tsaye.

Rumbun Labarai
Nijeriya na neman tallafin IMF da Bankin Duniya don rage tasirin yakin Iran kan tattalin arziki
Me ya sa hare-hare ke karu wa a Nijeriya duk da wanzuwar dakarun Amurka?
Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta soma bincike kan zargin kisan fararen-hula a kasuwar Jilli ta Yobe
ADC ta taya sabbin shugabannin jihohi murna, ta tsayar da ranar 12 ga Mayu don rantsar da su
Gwamnatin Nijeriya ta ba da umarnin soke fasfo ɗin mutanen da suka janye daga kasancewa ’yan ƙasar
Man fetur yana tsada sosai, amma mu gode wa Allah halin da muke ciki ya fi na wasu ƙasashe – Tinubu
An gano gawarwaki 61 bayan harin ta'addanci a jihar Neja ta Nijeriya
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda tare da ƙwace makamai a Jihar Filato
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce an kashe dakarunta a harin da Boko Haram ta kai hedkwatarsu a Borno
‘Gwarazan da ba za a iya mantawa da su ba’, Tinubu na juyayin kisan sojojin Nijeriya a harin Borno
Amurka ta bai wa jami'anta umarnin barin ofishin jakadancinta a Nijeriya saboda rashin tsaro a ƙasar
Aƙalla mutum 60 aka kashe a hare-hare daban-daban a arewa maso yammacin Nijeriya cikin mako guda
Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Nijeriya zai habaka a 2026
An mayar da 'yan Nijeriya 179 gida daga Libya
Babbar kotun Nijeriya ta ɗaure 'yanta'adda biyar
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda biyar, sun kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane a Filato
Matatar Dangote ta ƙara man da take turawa ƙasashen Afirka yayin da yaƙin Iran ya katse jigilar mai
An buƙaci Nijeriya ta gyara yadda ake bayar da labaran rikice-rikice
An kama mutum biyar kan harbin bindiga ba bisa ƙa’ida ba da 'ya kashe' yarinya Maiduguri a Nijeriya
Abin da ya sa Kano Pillars ta lallasa Bendel Insurance da ci 4-0 — Koci