‘Gwarazan da ba za a iya mantawa da su ba’, Tinubu na juyayin kisan sojojin Nijeriya a harin Borno

Shugaba Tinubu ya yi kira ga shugabannin dakarun sojin da ke fagen daga kada su karaya, yana mai ƙarfafa musu gwiwa da nuna godiya ga sadaukarwarsu wajen kare ƙasar.

By
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi juyayin sojojin da aka kashe a harin 'yanta'adda a Borno / User Upload


 Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana alhininsa game da kisan sojojin ƙasar, ciki har da kwamandansu Birgediya Janar Oseni Omoh Braimah a harin da ‘yanta’adda suka kai sansaninsu a garin Benisheikh na jihar Borno.

Shugaban ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga rundunar soji da iyalan sojojin da suka mutu, yana mai kira gare su ci gaba da jajircewa a duk da rashin da aka yin.

Hedikwatar tsaro ta ƙasar ta tabbatar da harin da mace-macen da suka faru da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Rundunar sojin ta ce masu ‘yanta’adda sun yi ƙoƙarin kutsawa cikin harabar sansanin sojim, amma dakarun Nijeriya sun daƙile su.

Ta ce sojojin “sun mayar da martani da jarumta da ba saba gani ba da ƙwarewa da kuma ƙarfin sojin mai yawa,” lamarin da ya tilasta wa maharan ja da baya.

Sai dai kuma, rundunar sojin ta tabbatar da cewa an kashe “wasu” sojoji a lokacin arangamar amma ba ta bayyana sunayensu ba.

A wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban Nijeriya ya fitar wadda shi ma shugaban ya wallafa a shafinsa na X, Shugaba Tinubu ya yaba da jarumtan dakarun, yana mai bayyana cewa sun yi yaƙi da ƙarfi domin daƙile harin ‘yanta’addan da kuma hana ‘yan Boko Haram shiga garuruwan da suke karewa.

Yayin da yake alhinin mutuwar sojojin, shugaban ya yi kira ga shugabannin dakarun sojin da ke fagen daga kada su karaya, yana mai ƙarfafa musu gwiwa da nuna godiya ga sadaukarwarsu wajen kare ƙasar.

“Rahotannin da na samu sun nuna cewa sojojinmu sun ƙaddamar da hare-hare ta sama da ta ƙasa babu ƙaƙƙautawa kan ‘yanta’addan, inda suka kassara da yawa daga cikin mayaƙansu da kwamandodinsu. Harin mayar da martani na masu tayar da ƙayar bayan, wata alama ce ta motsi-ya-fi-laɓewa

“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalan jarumai sojojinmu, bisa jagorancin Birgediya Janar Oseni Omoh Braimah, waɗanda suka sadaukar da kawunansu wajen kare ƙasarmu a jihar Borno.

“Gwamnatin ba za ta taɓa mantawa da sadaukar da kai da suka yi ba. Sadaukarwarsu ba za ta kasance a banza ba. "Saboda ƙarfin hali da sadaukarwar dakarunmu a fagen daga, aniyarmu ta kawar da ta'addanci da dukkan nau'ukan rikici a faɗin Nijeriya ta ƙarfafa fiye da yadda take a baya.

Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa: “Ina kira ga manyan kwamandodi da dakarunmu a duk fagen yaƙi, kada su karaya, kada ku gajiya. Hafsoshinmu da mazajenmu su ci gaba da hidima cikin mutunci da jarumta da kuma kishin ƙasa. Gwamnati za ta ci gaba da kasancewa tare da dakarun soji da bayar da kayayyakin aiki da kuma tabbatar da jin daɗin duk waɗanda suke sadaukar da rayukansu domin amincinmu.

“Ina yin kira ga duk ‘yan Nijeriya da kuma kafofin watsa labarai su ci gaba da tallafa wa sojinmu a yaƙin da suke babu ƙaƙƙautawa da masu tayar da ƙayar baya da fashin daji. Mu ƙaurace wa nuna farin ciki ko kuma lamuntar hare-hare kan dakarunmu. Waɗannan sojojin su ne gwarazanmu; waɗanda ba za a iya mantawa da su ba ko kuma a iya maye gurbinsu ba.

“Ina miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar Borno. Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki ga gwamnatin jihar domin samun cikakkiyar nasara da zaman lafiya mai ɗorewa,” in ji shugaban ƙasar.