Hukumar hana safarar mutane ta Nijeriya (NAPTIP) ta gano yunƙurin safarar mutane 1,508 tare da kama mutum 1,434 da ake zargi da hannu a safarar mutane tsakanin watan Agustan shekarar 2025 ya zuwa yanzu.
Darakta Janar ta NAPTIP, Binta Bello, ce ta bayyana wannan a zaman tuntuɓa na masu ruwa da tsaki kan Safarar Mutane a Nijeriya na 29 da taron matakin manufa na uku da aka yi a Abuja.
A wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook na NAPTIP ranar Talata, Bello ta ce hukumar ta kuma karɓi tare da kula da mutum 2,700 da lamarin ya shafa a lokacin, yayin da aka gabatar da batutuwa 65 da suka haɗa da mutum 85 a gaban kotu.

Ta ƙara da cewa batutuwa 74 sun yi silar samun mutum 97 da laifi na safarar mutane.
Darakta Janar ɗin ta ƙara bayyana cewa tun lokacin da aka kafa hukumar, NAPTIP ta ceto mutum 28,762 tare da tabbatar da cewa an samu mutum 857 da laifukan safarar mutane.
Ta bayyana cewa hukumar ta zafafa ƙoƙarinta kan amfani da fasaha wajen hana safarar mutane da yaudarar mutane ta intanet da kuma sauran hanyoyi na ci da gumin mutane tare da ƙarfafa tattara bayanan sirri da kare waɗanda lamarin ke rutsawa da su da haɗin kai na ƙasa da ƙasa.
Bello ta yi kira ga mataki na gaggawa na kafa rundunar NAPTIP ta Jiha a Jihar Delta, tana mai bayyana ta a matsayar jiha ɗaya tilo wadda ba ta da runduna ta hukumar.
Ta ce rundunar za ta ƙarfafa mayar da martani na aiki da kuma inganta kare waɗanda lamarin yake rutsawa da su a jihar.
A wani ɓangaren kuma, Gwamnatin Tarayyar Nijeirya ta sake tabbatar da jajircewarta ga ƙarfafa martanin Nijeriya ga safarar mutane ta hanyar inganta tallafi na hukuma da goyon bayan na manufa da samar da isasshen kuɗi ga NAPTIP da sauran masu ruwa da tsaki.
Antoni Janar kuma Ministan Shari’a na ƙasar Lateef Fagbemi, SAN, ne ya ba da wannan tabbacin yayin da yake buɗe taron.
Ministan da ya sami wakilcin Muƙaddashin Daraktan Ɓangaren ‘Yancin ‘yan ƙasa na ma’aikatar Shari’a, Kabiru Haliru, ya yaba wa NAPTIP da abokan aikinta bisa nasarorin da suka samu wajen gurfanar da masu safarar mutane da ceto waɗanda ake safara da kula da su da wayar da kan jama’a da kuma samar da manufofi.
Ya jaddada buƙatar da ke akwai ta jajircewar siyasa mai ɗorewa da ayyukan haɗin gwiwa masu ƙarin ƙarfi da kuma isassun kayayyaki aiki na daƙile safarar mutane.





















