Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane ta Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama aƙalla mutum biyar da ake zargi da safarar mutane tare da kuɓutar da mutum 24 a filin jiragen saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe International Airport, da ke Abuja.
Jami’in watsa labaran hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ya bayyan a ranar Laraba cewa a cikin waɗanda aka kama akwai wani mutum da ya yi yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa game da ƙaruwar safarar mutane da ake samu, musamman a lokacin da ake samun yawan ‘yan Nijeriya ke barin ƙasar.
Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello.
Ya bayyana cewa a cikin waɗanda ake zargin akwai wani babban jami’in tsaro, wanda ke cikin masu safarar mutane a kudu maso yammacin Nijeriya.
Adekoye ya ce waɗanda aka kuɓutar ɗin yara ne da matasa waɗanda shekarunsu ke tsakanin shekara 15 zuwa 26 waɗanda aka ɗauko daga jihohin Kano da Katsina da Oyo da Ondo da kuma Ribas, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa ƙasashen Iraƙi da Sudan da Masar da Saudiyya da Bahrain da kuma Afghanistan.
Ɗaya daga cikinsu ta sha alwashin cewa sai ta tabbatar an gurfanar da mahafinta a gaban kotu kan yunƙarin safararta da ya yi zuwa iraƙi, in ji jami’in.
Ya ƙara da cewa wata cikin waɗanda aka yi ƙoƙarin safarar ta ce mahafiyarta ce ta rinjaye ta ta yarda da cewa za ta tafi Turai domin yin aiki ta samu daloli.