| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya ta fara kwashe 'yan ƙasarta daga Iran
Abike Dabiri ta bayyana cewa jami'an Nijeriya suna jira a kan iyaka domin karɓar 'yan ƙasar da ke tserewa daga yaƙin Iran, tana mai ƙarawa da cewa kawo yanzu babu ɗan Nijeriya da ya mutu a yaƙin.
Gwamnatin Nijeriya ta fara kwashe 'yan ƙasarta daga Iran
Abike Dabiri-Erewa, shugabar hukumar da ke kula da 'yan Nijeriya da ke ƙetare / User Upload

Gwamnatin Nijeriya ta fara kwashe ‘yan ƙasarta daga Iran, inda jami’ai ke musu rakiya daga kan iyakar Armenia yayin da yaƙin Amurka da Isra’ila kan Tehran ke ci gaba da ƙamari.

Shugabar hukumar da ke kula da ‘yan Nijeriya da ke ƙasashen waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X ranar Talata, ta ce ana raka ‘yan ƙasar da ke son barin ƙasar Iran ta hanyar kan iyaka.

Ta kuma bayyana cewa jami’an Nijeriya suna jira a kan iyaka domin tarbar ‘yan ƙasar da ke tserewa daga yaƙin Iran, tana mai ƙarawa da cewa ba a samu wani ɗan Nijeriya da ya mutu a yaƙin ba.

“Jami’an ofishin jakadancin Nijeriya a Iran suna raka duk wani ɗan ƙasar da ke son tafiya gida zuwa kan iyakar Armenia domin samun damar wucewa cikin aminci.

Masu AlakaTRT Afrika - Rikicin Gabas ta Tsakiya ya tilasta wa jiragen ruwa na duniya sauya hanya suna bi ta Afirka

“Babu wani ɗan Nijeriya a Iran da yaƙin ya shafa amma jami’anmu suna kan iyaka domin tarbar duk wanda ke son tafiya,” in ji ta.

Ba ta ba da haƙiƙanin adadin ‘yan Nijeriya da ke Iran ba ko kuma adadin waɗanda aka riga aka kwashe.

Matakin na kuɓutar da ‘yan Nijeriyar na zuwa ne kwanaki 11 da fara yaƙin da ya kashe mutum fiye da 1,300, tare da jikkata da kuma raba wasu mutane da gidajensu.

Ma’aikatar lafiyar Iran ta ce hare-haren Amurka da Isra’ila sun kashe fiye da mutum 1,300 a Iran, inda fiye da mutum 12,000 suka jikkata.

Iran ta ce mata 200 na cikin waɗanda aka kashe, ciki har da yara mata ‘yan makarantar Minab 168.

Kazalika, kimanin ma’aikatan jinya 55 sun jikkata yayin da aka kashe 11 daga cikinsu.

Rumbun Labarai
'Yanbindiga sun kai hai wani gidan marayu a Jihar Kogi sun sace yara 23 amma an ceto 15
Jakadan Saudiyya a Nijeriya ya gana da Dangote don inganta kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu
Shugaban Nijeriya ya nuna goyon baya ga kasashen Gulf game da yaƙin Iran
Babbar Alƙaliyar Nijeriya ta gargaɗi kafafen yaɗa labarai da su guji ƙarin gishiri a rahotanni
Tinubu ya nemi izinin majalisar dattawan Nijeriya don karɓo bashin $516m a gina titin Sokoto-Badagry
Tinubu ya cim ma yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama domin hana shirinsu na dakatar da aiki
Sojojin Nijeriya sun kashe mayakan ISWAP da dama a yankin Tafkin Chadi
Aƙalla mutum 23 ‘yanta’adda da ‘yanbindiga suka kashe a hare-hare daban-daban a arewacin Nijeriya
CBN ta gargadi 'yan Nijeriya kan yunƙurin masu kutse cikin asusun bankunan mutane
Dimokuraɗiyya za ta ɗore duk da barazanar da take fuskanta – Tinubu
An samu bullar Covid-19 a Nijeriya shekaru bayan duniya ta yi fama da ita
Tinubu ya sauke Ministan Kuɗi Edun Wale Edun da na Gidaje Ahmad Dangiwa ya ba da sunan wasu sabbi
Sojojin saman Nijeriya sun kashe tarin 'yan-ta'adda a dajin Sambisa
Nijeriya za ta gurfanar da janar mai ritaya da tsohon minista a kotu kan tuhumar su da juyin mulki
A karon farko Nijeriya ta fitar da mai fiye da wanda ta shigar cikin ƙasar
Dakarun Nijeriya sun kama masu kai wa 'yanta'adda makamai a Jihar Kogi
Dalilai uku na ɗage shari'ar tabbatar da Sarkin Kano a Kotun Ƙolin Nijeriya
NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin kwanon abinci a filin jirgin saman Legas
Farashin saniya ya kai naira N2.5m, fiye da farashin mota a Legas, in ji mahauta
Wasu na da hannu a kashe-kashe domin neman shugabanci – Ministan Tsaron Nijeriya