Hare-haren ƙunar-baƙin-wake sun kashe mutum aƙalla 23 a birnin Maiduguri na Nijeriya

An kai hare-haren ne a ƙofar shiga Asibitin Koyarwa na Jami'ar Maiduguri da Monday Market da kuma gidan waya da ke birnin.

By
An ji ƙarar fashewar abubuwa a birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Nijeriya, in ji majiyoyin tsaro da na mazauna birnin / Reuters

Mutum aƙalla 23 ne suka mutu yayin da mutum 146 suka jikkata a hare-haren ƙunar-baƙin-wake a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya ranar Litinin da dare, a cewar hukumomi.

Bamabaman sun tashi ne a ƙofar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da Monday Market da kuma gidan wayan da ke birnin.

Jaridar Daily Trust ta ambato Surajo Abdullahi, shugaban yanki na hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA yana tabbatar mata cewa mutum aƙalla 23 ne suka mutu sannan mutum 169 suka jikkata a hare-haren.

“A halin yanzu mutum 108 suna samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, kuma 20 suna Asibitin Tunawa da Umaru Shehu yayin da mutum 17 ke Asibitin Ƙwararru na Maiduguri,” in ji shi.

Mazauna Maiduguri da dama sun ce a shekarun baya birnin ya fara mantawa da hare-haren bamabamai da harbe-harben bindigogi amma yanzu lamura sun soma dagulewa.

“Komai ya dawo sabo yanzu – muna cikin tsoro da fargaba tare da ganin jini a ƙasa. Waɗannan hare-hare sun nuna yadda birnin na Maiduguri ke sake fama da tashin hankula bayan sun lafa a shekarun baya,” in ji wani mazaunin birnin.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan Jihar Borno ASP Nahum Kenneth Daso ya ce ana tunanin hare-haren ƙunar-baƙin-wake suka haddasa tashin bama-baman.

Sai dai ya ce abubuwa sun koma yadda ake a da a wuraren, yana mai kira ga mutane su bai wa ‘yansanda rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba.

‘Matsorata’

Kazalika rundunar sojin Nijeriy ta bayyana hare-haren na ƙunar-baƙin-wake a matsayin na matsorata kuma ragwaye.
A wata sanarwar da ya fitar ranar Litinin, jami’in watsa labarai na Operation Haɗin, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce hare-haren sun mayar da hankali ne kan wuraren da mutane ke taruwa da yawa a wani yunƙuri na ‘yanta’adda na kashe mutane da yawa da kuma tayar wa mutane hankali a cikin birnin.

“Dakarun Operation HADIN KAI, tare da ɓangaren kawar da bama-bamai na rundunar ‘yansandan Nijeriya (EOD) da sauran rundunonin tsaro sun mayar da martani da wurwuri game da lamarin inda suka toshe wuraren da lamarin ya shafa nan-take domin hana ƙarin lahani,” in  ji sanarwar.

“Bayanai na farko-farko da aka samu sun nuna cewa mai yiwuwa ‘yanta’addan sun tura wasu ‘yan ƙunar-baƙin-wake cikin Maiduguri da zummar ƙaddamar da hare-hare a wurare masu tarin jama’a, in ji Laftanar Kanal Sani Uba.

“Saboda haka dakarun tsaro sun ƙarfafa sa ido da sintiri da kuma matakan warware abubuwa masu fashewa a faɗin birnin domin kama sauran waɗanda ake zargi da kuma hana ƙarin hare-hare,” in ji shi.