Wasu da ake zargin ‘yanta’adda ne sun kai hari da daddare kan wani sansanin sojojin Nijeriya a wajen birnin Maiduguri, karo na farko cikin shekaru a babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar, kamar yadda ‘yansanda, jami’an agaji da mazauna yankin suka bayyana a ranar Litinin.
‘Yanta’addan Boko Haram da kuma kungiyar ISWAP sun ƙara ƙaimi wuri kai hare-hare kan sansanonin sojoji a arewa maso gabashin Nijeriya a ‘yan kwanakin nan.
Yaƙin da ake yi da ‘yanta’addan na tsawon shekaru 16 a ƙasar ya kashe mutane fiye da 40,000 tare da raba kusan mutane miliyan biyu da muhallansu.
Harın ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na dare a unguwar Ajilari Cross, wata unguwa a kudu maso yammacin Maiduguri, wadda ke da nisan kilomita kaɗan daga filin jirgin saman birnin.
Mazauna yankin da jami’an agaji sun ce sojoji sun yi gaggawar fatattakar maharan.
Unguwar ta kasance cikin kwanciyar hankali a safiyar Litinin, kamar yadda ‘yan jaridar kamfanin dillancin labarai na AFP suka shaida.
Mai magana da yawun ‘yansanda, Nahum Kenneth Daso, ya wallafa a shafinsa na X cewa an samu rahoton “hare-haren da ake zargin ‘yanta’addan BH/ISWAP ne suka kai amma aka daƙile a Ajilari Cross”. Ya kuma tabbatar da wani lamari daban inda jami’an tsaro suka daƙile wani “yunkurin harin ta’addanci” a Ƙaramar Hukumar Damboa, da ke kudancin Maiduguri.
Wani mai magana da yawun jami’an agaji a jihar Borno ya shaida wa AFP cewa sun samu “rahotannin hare-hare” daga ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai amma sojoji sun fatattake su, kuma ba a samu asarar rayukan fararen-hula ba.
Mazauna yankin sun ce an samu mutuwar mutum huɗu daga ɓangaren maharan.
“Da misalin ƙarfe 12:15 na dare yau, mun fara jin ƙarar harbe-harbe daga sansanin sojoji. Daga baya muka fahimci cewa ‘yanta’adda ne, waɗanda ake zargin Boko Haram ne suka kai harin,” in ji wani mazaunin Ajilari Cross, Mustapha Aminu a tattaunawarsa da AFP.
“Mun kirga gawarwaki huɗu na maharan,” in ji shi.
Wata mazauniyar yankin, Yakaka Ali Gana, ta ce: “Wannan ne karo na farko da maharan suka shigo cikin al’ummarmu suka kai hari kan sansanin sojoji.”
Har yanzu rundunar sojoji ba ta yi tsokaci ba.
A da Maiduguri ya kasance wurin da ake yawan kai hare-hare da tayar da bama-bamai, inda hare-haren suka fi ƙamari a tsakiyar shekarun 2010, amma a ‘yan shekarun nan birnin ya kasance cikin kwanciyar hankali.







