Enas Arbab ta tsere daga yankin yammacin Sudan na Darfur bayan dakarun RSF sun ƙwace garinsu, inda ta riƙe ɗanta mai shekara ɗaya da kuma tunanin mahaifinta wanda aka kashe, a cewarta, kawai domin ya yi aiki a wurin dafa abinci na sadaka domin bai wa ‘yan gudun hijira.
Dakarun RSF da ke yaƙi da sojin Sudan tun watan Afrilun shekarar 2023 — sun yi wa Al Fasher a yankin yammaci na Darfur ƙawanya, inda suka jefa mutane cikin matsananciyar yunwa kafin su ƙwace birnin.
Jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) sun ce dubban fararen-hula ne aka kashe yayin da RSF ta ƙwace Al Fasher a watan Oktoba. Kashi 40 cikin 100 na mutanen birnin 260,000 ne suka tsere daga harin, waɗanda dubbansu sun jikkata, in ji jami’ai. Ba a san abin da ya faru da sauran ba kawo yanzu.
Yayin yaƙin, Arbab ta ce mayaƙan RSF sun ɗauke mahaifinta, Mohamed ِArbab, daga gidansu inda suka yi ta dukansa a gaban iyalinsa, kuma suka nemi kuɗin fansa. Yayin da iyalansa suka kasa biya, sun shaida musu cewa sun kashe shi, in ji ta. Kawo yanzu iyalansa ba su san inda gawarsa take ba.
A lokacin da mijinta ya ɓata bayan wata ɗaya, Enas Arbab ta yanke shawarar tserewa ta arewa, zuwa Masar. “Mun kasa zama a Al Fasher," in ji ta. " Babu tsaro a wurin kuma babu abinci ko ruwa.”
Mahaifinta ɗaya ne daga cikin ma’aikata fiye da 100 na wuraren dafa abinci domin bayarwa da aka kashe tun lokacin da aka fara yaƙin, in ji ma’aikatan da suka yi magana da kamfanin dillancin labaran The Associated Press da kuma ƙungiyar Aid Workers Security database, mai sa ido kan muhimman ababen da ke shafar ma’aikatan jinya a duniya .
A wuraren da yaƙi ya yi tsanani — musamman a Darfur — tamowa na yaɗuwa kuma abinci da abubuwan rayuwa na yau da kullum sun yi ƙaranci. Wuraren dafa abincin da mutanen gari ke jagoranta sun zamanto wani taimako na ƙarshe da ya yi saura ga mutane, amma an sace ko yi fashi ko daka ko kuma kashe da yawa daga cikin ma’aikatan wuraren.
Alƙaluma masu sosa rai a wani yaƙin basasa mara tausayi
Ɗan aikin sa-kai Salah Semsaya da ke aiki da ƙungiyar ba da taimakon gaggawa ta Emergency Response Rooms — wata ƙungiya da ta fito a matsayar tsari na cikin gida kuma a halin yanzu tana aiki a larduna 13 a faɗin Sudan, da ‘yan sa-kai 26,000 — ya bayyana haɗuran da ma’aikata ke fuskanta a wuraren dafa abinci domin bayarwa kyauta.
Asalin adadin ma’aikata da aka kashe zai iya zarce 100 da aka yi kiyasi, in ji shi, amma yaƙin ya hana tattara sahihan bayanai da kuma adana bayanan.
Semsaya ya ba da alƙaluma da ke nuna cewa kashi 57 cikin 100 na kashe-kashen da aka tabbatar na ma’aikatan wuraren dafa abincin sun faru ne a Khartoum, mafi yawanci, yayin da babban birnin Sudan ɗin yake ƙarƙshin ikon rundunar RSF, kafin soji ta sake karɓar sa a watan Maris da ya gabata. Aƙalla kashi 21 cikin 100 na kashe-kashen an yi su ne a Darfur.
Sama da 50 cikin waɗanda aka kashe a Khartoum sun yi aiki ne da ƙungiyarsa, in ji Semsaya .
Yaƙin basasan Sudan ya ɓarke ne bayan tayar da jijiyar wuya tsakanin sojin ƙasar da rundunar RSF ya taɓarɓare zuwa rikicin da aka fara a Khartoum kuma ya baza faɗin ƙasar.
Ana yawan kai wa ma’aikatan jinya hari.
Dan Teng’o, jami’an watsa labaran ofishin MDD kan harkar jinƙai, ya ce babu tabbaci kan ko ana far ma ma’aikatan wuraren dafa abincin kyauta saboda aikinsu ko kuma saboda yadda ake ganin suna da alaƙa da wani ɓangare na yaƙin.
Ma’aikatan wuraren dafa abincin sanannu ne a cikin al’ummominsu saboda aikin da suke yi, lamarin da ya sa ake kai musu hare-hare cikin ruwan sanyi, in ji masu fafatuka.
Kuɗaɗen fansan da ake nema sun kama ne daga $2,000 zuwa $5,000, lamarin da ke ƙaruwa da zaran iyalai sun biya daga cikin kudin fansan.
“A bayyane yake cewa taɓarɓarewar tsaro... ya yi tasiri sosai a kan al’ummomin ƙasar, ciki har da ‘yan sa-kai da ke tallafa wa wuraren dafa abinci na al’umma,” in ji Teng’o.












