CAF ta ce za ta 'ɗauki matakan da suka dace' bayan abubuwan da suka faru a wasan ƙarshe na AFCON

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka, CAF, ta faɗa a ranar Litinin cewa za ta ɗauki "matakan da suka dace" kan "waɗanda aka samu da laifi" bayan abubuwan mamaki da suka mamaye wasan ƙarshe na Gasar Kofin Ƙwallon Kafa ta Afirka.

By
CAF ta yi Allah wadai da al'amuran hargitsi da aka gani yayin wasan karshe na AFCON 2025 tsakanin Morocco da Senegal a ranar 18 ga Janairu, 2026. / Reuters

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka, CAF, ta faɗa a ranar Litinin cewa za ta ɗauki "matakan da suka dace" kan "waɗanda aka samu da laifi" bayan abubuwan mamaki da suka mamaye wasan ƙarshe na Gasar Kofin Ƙwallon Kafa ta Afirka.

Sai dai CAF ba ta ɗaura laifi kan kowa tsakanin Senegal ko Morocco ba.

A wasan ƙarshe na ranar Lahadi, yawancin 'yan wasan Senegal sun fita daga fili a matsayin nuna rashin amincewa, lokacin da alƙalin wasa Jean-Jacques Ndala ya bai wa masu masaukin baƙi Maroko bugun daga kai sai mai tsaron gida, a cikin lokacin da aka ƙara, yayin da aka kammala wasan 0-0.

Wasu magoya bayan Senegal sun yi arangama da jami'an tsaro na Maroko a wani ɓangare na filin wasa a Rabat.

Nazarin bidiyo

Bayan 'yanwasan sun koma filin wasa, mai tsaron ragar Senegal Edouard Mendy ya tare bugun panaretin da aka buga sannan Senegal ta ci samu nasara a wasan da ci ɗaya 1-0 a ƙarin lokacin da aka yi.

"Hukuma ƙwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta yi Allah wadai da irin wannan halayyar da ba za a amince da ita ba daga wasu 'yanwasa da jami'ai yayin wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Afirka 2025 tsakanin Maroko da Senegal a Rabat daren jiya," in ji sanarwar tasu.

"CAF ta yi Allah wadai da kowace irin mummunar ɗabi’a da ta faru yayin wasanni, musamman waɗanda suka yi ta kai farmaki ga tawagar alƙalai ko masu shirya wasa."

"CAF na nazarin dukkan bidiyoyin, kuma za ta miƙa al'amarin ga hukumomin da suka dace domin a ɗauki matakin da ya kamata kan waɗanda aka same su da laifi."

Nasara a ƙarin lokaci

Daga ƙarshe dai 'yanwasan Senegal sun koma filin wasa bayan tsohon ɗanwasan Liverpool Sadio Mane, ɗaya daga cikin 'yan tawagarsu da suka tsaya a filin, ya roƙe su su dawo.

Brahim Diaz na Morocco, shi ne ya samu damar bugun na daga kai sai mai tsaron gida, sai dai ya buga ƙwallon hannun mai tsaron gida na Senegal Edouard Mendy.

Senegal ta samu nasara a wasan ƙarshe ta hannun Pape Gueye inda ya jefe ƙwallo mai ban mamaki a ragar Maroko a cikin ƙarin lokacin da aka yi.