| Hausa
AFCON 2025
2 minti karatu
Senegal ta doke Maroko da ci 1-0 a zazzafan wasan ƙarshe na gasar AFCON
Bayar da bugun fenareti ga Morocco da ta karbi bakuncin gasar a mintuna na karshe na wasan ya sanya ‘yan wasan Senegal fita daga fili don nuna rashin amincewa, amma bayan Terenga Lions sun dawo filin, Brahimi Diaz ya zubar da fenaretin.
Senegal ta doke Maroko da ci 1-0 a zazzafan wasan ƙarshe na gasar AFCON
Wannan ne karo na biyu da Senegal ta lashe gasar AFCON bayan ta lashe a 2021. / Reuters / Reuters
21 awanni baya

Senegal ta ɗauki kofin AFCON bayan ta doke Maroko da ci 1-0 a fafatawa mai zafi da suka yi ranar Lahadi a Rabat, babban birnin ƙasar.

Bayar da bugun fenareti ga Maroko da ta karɓi baƙuncin gasar AFCON 2025 a mintuna na ƙarshe na wasan ya sanya ‘yanwasan Senegal fita daga fili don nuna rashin amincewa, amma bayan Terenga Lions sun dawo filin, Brahimi Diaz ya zubar da fenaretin.

Wasan ya ƙare ba tare da wata ƙungiya ta jefa ƙwallo ba.

Pape Gueye na Senegal ne ya zura ƙwallo a wasan a minti na 94 na ƙarin lokaci don lashe gasar AFCON a karo na biyu bayan lashe wa a karon farko a 2021.

Alƙalin tsakiya ya ƙi amincewa da yunƙurin Senegal na farko na nuna rashin amincewa da bugun fenareti, wanda ya bayar da bugun fenareti bayan an kayar da wani ɗan wasan Maroko a gaf da ragar Senegal.

An tabbatar da hukuncin bugun fenareti bayan wani mataimakin alkalin wasa na bidiyo (VAR) ya sake duba laifin da aka yi.

Diaz na Maroko ne ya buga fenaretin amma mai tsaron gida na Senegal Edouard Mendy ya cafe ƙwallon.

Senegal ta ci gaba da riƙe jagorancinta da ci 1-0 har zuwa lokacin da aka kammala gasar a ƙarin lokaci.