Ƙasashe fiye da 20 sun yi Allah wadai da RSF kan kashe-kashen da take yi a Sudan

Ƙasashen da suka yi Allah wadai da RSF sun haɗa da Canada, Sifaniya, Birtaniya, Norway, Jamus, Ireland, Sweden, Austria, Croatia, Jamhuriyar Czech, Finland, Poland da Switzerland.

By
Hukumar da ke kula da masu ƙaura ta duniya (IOM) ta ce an raba kusan mutum 89,000 daga gidajensu a Al Fasher da kewayensa a Arewacin Darfur tun Oktoba

Wata ƙungiya ta ministocin harkokin waje da manyan jami'ai daga ƙasashe fiye da 20 ta fitar da wata sanarwa ta haɗin-gwiwa a ranar Litinin inda ta yi Allah wadai da cin zarafi da kuma keta dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa da rundunar RSF ke yi a Sudan, ta bayyana "matuƙar fargaba game da rahotannin cin zarafi da aka aikata kan fararen-hula".

Sanarwar ta bayyana cewa jami’an “sun yi matuƙar firgita game da rahotannin ci gaba da cin zarafin fararen-hula a lokaci da kuma bayan ƙwace birnin El-Fasher da Rundunar kai Ɗaukin Gaggawa (RSF) ta yi”, da kuma ƙaruwar yaƙe-yaƙe a faɗin Arewacin Darfur da yankin Kordofan.

Kazalika sanarwar ta bayyana cewa da “gangan ake kai wa fararen-hula hare-hare, da kuma kisan gillar da aka yi wa al'umma, da cin zarafin mata ta hanyar lalata, ga kuma yunwa a matsayin makamin yaƙi da toshe hanyoyin samun agajin jinƙai” waɗanda gabaki ɗaya suke a matsayin "keta dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa".

"Irin waɗannan ayyuka, idan an tabbatar da su, sun ƙunshi laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil'adama a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa," in ji sanarwar.

Ministocin da kuma jami’an sun buƙaci a kawo ƙarshen tashin hankalin nan-take, suna masu cewa "dole ne a kawo ƙarshen rashin adalci tare da tabbatar da an bi gaskiya".

Sun jaddada cewa "kariya da adalci ga al'ummar Sudan ba kawai iya shari'a suka tsaya ba, sun zama muhimman abubuwan da ake matuƙar buƙata’’.

Sanarwar ta kuma bayyana yanayin a matsayin "abin da ba za a iya jurewa ba la’akari da yadda yunwa ke ƙara tsanani saboda katse hanyoyin shigar da tallafin abinci,” sun yi kira ga hukumomi da su bai wa Hukumar Abinci ta Duniya (WFP), da Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) da sauran hukumomin agaji damar isar da tallafi cikin ‘yanci.

"Dole ne dukkan ɓangarorin su mutunta dokar jinƙai ta duniya," in ji sanarwar, tana mai kira da a samar da tsaro ga fararen-hula da kuma sauƙaƙa hanyoyin kai tallafi nan-take bisa ga ƙudurin Majalisar Tsaro ta MDD mai lamba 2736.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga ɓangarorin da ke yaƙi da juna da su amince da yarjejeniyar tsagaita wuta tare da ajiye makamansu, sannan ta yi gargaɗi game da duk wani yunƙuri na raba Sudan.

"Muna sake jaddada goyon bayanmu ga 'yancin kai, da haɗin kai da kuma haƙƙin 'yan ƙasa na rayuwa cikin zaman lafiya, mutunci da adalci ba tare da tsangwama daga waje ba," a cewar sanarwar.

Daga cikin ƙasashen da suka yi Allah wadai da RSF sun haɗa da Canada, Sifaniya, Birtaniya, Norway, Jamus, Ireland, Sweden, Austria, Croatia, Jamhuriyar Czech, Finland, Poland da Switzerland.

Ministocin da jami'ai sun kammala da yin kira ga dukkan ɓangarorin da su "haɗu kan teburin tattaunawa", suna mai jaddada cewa "tsarin siyasa mai faɗi na Sudan kana wanda ya haɗa kowa ne kawai zai iya magance ƙalubalen ƙasar".

A ranar Lahadi, Ƙungiyar Kula masu gudun hijira ta Duniya (IOM) ta ba da rahoton cewa kusan mutane 89,000 ne suka rasa matsugunansu daga Al Fasher da kewayenta a Arewacin Darfur tun daga 26 ga Oktoba, ranar da RSF ta ƙwace iko da birnin.

 RSF ta ƙwace iko da Al-Fasher kuma ta aikata kisan ƙare-dangi, a cewar ƙungiyoyin cikin gida da na ƙasashen waje, wanda ya zo a daidai lokacin da aka yi gargaɗin cewa harin zai iya janyo raba ƙasar.

Tun daga ranar 15 ga watan Afrilun 2023, rundunar sojojin Sudan da na RSF suka tsunduma yaƙi inda har yanzu kokarin kawo ƙarshensa ko kuma sasantawa daga yankin da ma ƙasashen duniya ya ci tura.

Rikicin ya kashe dubban mutane tare da raba miliyoyin wasu da muhallinsu.