| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Amurka ta ƙaƙaba wa wasu 'yan Nijeriya takunkumi kan zargin ta'addanci da laifuka ta intanet
Daga cikin waɗanda aka ƙaƙaba wa takunkumin kuma aka ƙwace kadarorinsu sakamakon alaƙa da ƙungiyoyin 'yanbindiga su ne manyan waɗanda ke da alaƙa da Boko Haram da ISWAP da kuma Ansaru.
Amurka ta ƙaƙaba wa wasu 'yan Nijeriya takunkumi kan zargin ta'addanci da laifuka ta intanet
Wasu daga cikin 'yan Nijeriya da gwamnatin Trump ta sanya wa takunkumi suna da alaƙa da Boko Haram da ISWAP da kuma Ansaru. / AP
17 Fabrairu 2026

Gwamnatin Amurka ta ƙaƙaba takunkumai kan wasu ‘yan Nijeriya 18 da wasu ƙungiyoyi kan zargin ta’addanci da laifuka ta intanet da safarar miyagun ƙwayoyi.

Wannan na zuwa ne yayin da Washington ke ƙarfafa haɗin kai na soji da Nijeriya domin daƙile barazanar masu tsattsauran ra’ayi.

A ƙarƙashin shirye-shiryen da ofishin Amurka da ke kula da kadarori na ƙetare (OFAC), an ayyana ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi a wani mataki na musamman mai nuna aikata ta’addanci a duniya (SDGT) da jerin barazana masu alaƙa da intanet (CYBER2) da kuma safarar ƙwayoyi (SDNTK).

Boko Haram da ƙungiyoyi masu alaƙa da IS

A cikin waɗanda aka ƙaƙaba wa takunkumi kuma aka ƙwace kadarorinsu sakamakon alaƙa da ƙungiyoyin ‘yanbindiga akwai manyan waɗanda ke da alaƙa da Boko Haram da ISWAP da Ansaru — ƙungiyoyin da suka shafe fiye da shekara goma suna kai hare-hare a arewa maso gabashin Nijeriya.

Cikin waɗanda aka sanya sunayensu a jerin sunayen ‘yanta’adda na duniya akwai tsohon shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau da kwamandoji masu alaƙa da ISIS Abu Musab al-Barnawi da Khalid al-Barnawi, tare da wasu masu hulɗa da su da ke da alaƙa da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

Masu AlakaTRT Afrika - Sojojin Amurka sun isa arewa maso gabashin Nijeriya

Har wa yau akwai Salih Yusuf Adamu da Ibrahim Ali Alhassan da Surajo Abu Bakr Muhammad da Abdurrahman Ado Musa da Ali Abbas Usman Jega.

Kazalika an ƙaƙaba wa reshen Nijeriya na ƙungiyar RIHS mai rajin farfaɗo da Islama domin zargin taimaka wa ayyukan masu tsattsauran ra’ayi.

Takunkumai masu alaƙa da laifukan intanet da safarar ƙayoyi

A wani mataki na daban, an bayyana sunayen wasu ‘yan Nijeriya biyar — wani da ake ce wa Nnamdi Orson Benson da Abiola Ayorinde Kayode da Alex Afolabi Ogunshakin da Micheal Olorunyomi da kuma Richard Izuchukwu Uzuh — a ƙarƙashin dokar hana laifukan intanet ta Amurka US CYBER2 bisa rawar da ake zargin sun taka a wajen shirya manyan damfara ta intanet.

Mutane biyu, wani mai suna Wole A. Ogungbuyi da Babestan Oluwole Ademulero, kuwa an ayyana su a matsayin gaggan masu safarar miyagun ƙwayoyi kan zargin da aka yi musu na kasancewa cikin masu safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasashen duniya.

Rumbun Labarai
Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta soma bincike kan zargin kisan fararen-hula a kasuwar Jilli ta Yobe
ADC ta taya sabbin shugabannin jihohi murna, ta tsayar da ranar 12 ga Mayu don rantsar da su
Gwamnatin Nijeriya ta ba da umarnin soke fasfo ɗin mutanen da suka janye daga kasancewa ’yan ƙasar
Man fetur yana tsada sosai, amma mu gode wa Allah halin da muke ciki ya fi na wasu ƙasashe – Tinubu
An gano gawarwaki 61 bayan harin ta'addanci a jihar Neja ta Nijeriya
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda tare da ƙwace makamai a Jihar Filato
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce an kashe dakarunta a harin da Boko Haram ta kai hedkwatarsu a Borno
‘Gwarazan da ba za a iya mantawa da su ba’, Tinubu na juyayin kisan sojojin Nijeriya a harin Borno
Amurka ta bai wa jami'anta umarnin barin ofishin jakadancinta a Nijeriya saboda rashin tsaro a ƙasar
Aƙalla mutum 60 aka kashe a hare-hare daban-daban a arewa maso yammacin Nijeriya cikin mako guda
Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Nijeriya zai habaka a 2026
An mayar da 'yan Nijeriya 179 gida daga Libya
Babbar kotun Nijeriya ta ɗaure 'yanta'adda biyar
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda biyar, sun kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane a Filato
Matatar Dangote ta ƙara man da take turawa ƙasashen Afirka yayin da yaƙin Iran ya katse jigilar mai
An buƙaci Nijeriya ta gyara yadda ake bayar da labaran rikice-rikice
An kama mutum biyar kan harbin bindiga ba bisa ƙa’ida ba da 'ya kashe' yarinya Maiduguri a Nijeriya
Abin da ya sa Kano Pillars ta lallasa Bendel Insurance da ci 4-0 — Koci
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda yaran Ado Aleiro
‘Yanta’adda sun kai hari ofishin ‘yansanda a Borno, sun kashe jami’ai huɗu