| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Amurka sun isa arewa maso gabashin Nijeriya
Jami'ai a Hedikwatar Tsaron Nijeriya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa kimanin sojojin Amurka 100 sun isa Nijeriya tsakanin Alhamis da Lahadi a matsayin sannan ƙarin jirage na tafe a mako mai zuwa.
Sojojin Amurka sun isa arewa maso gabashin Nijeriya
A halin yanzu, Nijeriya ta ƙara matakan tsaro na cikin gida, yayin da rundunar soji ta sanar da tura dakaru na musamman zuwa Jihohin Filato da Taraba / AA
16 Fabrairu 2026

Jiragen rundunar sojin Amurka uku masu ɗauke da sojoji da makamai sun isa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a Nijeriya, wanda hakan wata alama ce ta sabuwar alaƙar soji da tsaro wadda za ta mayar da hankali kan tallafi na tsaro, in ji jami’a.

Jami'ai a Hedikwatar Tsaron Nijeriya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa kimanin sojojin Amurka 100 sun isa Nijeriya tsakanin Alhamis da Lahadi a matsayin wani ɓangare na tura rukunin farko, tare da karin jirage da ke tafe a makonni masu zuwa.

"Kamar yadda aka bayyana a makon da ya gabata, sojojin Amurka za su mayar da hankali kan ayyukan da ba na yaki ba kuma za su yi aiki daga cibiyoyin bayar da marni. Aikin su shi ne tallafa wa kokarinmu a nan," in ji wani jami'i da ya nemi a sakaya sunansa a tattaunawarsa da Anadolu a ranar Litnin.

Masu AlakaTRT Afrika - Amurka za ta tura sojojinta 200 Nijeriya

A cikin bayanan da Anadolu ta ruwaito a baya, Manjo Janar Samaila Uba, mai magana da yawun Hedikwatar Tsaron Nijeriya, ya bayyana cewa ma'aikatan Amurka "ba sa aiki a matsayin masu yaƙi kuma ba za su shiga aiki kai tsaye ba.”

Caccakar Amurka

Wannan matakin ya zo ne a yayin da ake samun ƙarin matsin lamba daga shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya soki yadda Nijeriya ke tafiyar da martani ga hare-haren da ake kai wa al'ummomin Kirista.

Gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da wannan ikirari, inda take cewa al'ummomin Kirista sun sha fuskantar hare-hare masu halaka rayuka, haka kuma fararen-hula Musulmai su ma ana kashe su da yawa a cikin rikicin da ke ci gaba.

A halin yanzu, Nijeriya ta ƙara matakan tsaro na cikin gida, yayin da rundunar soji ta sanar da tura dakaru na musamman zuwa Jihohin Filato da Taraba, waɗanda suka sha fama da tashin hankali akai-akai.

Yayin da jami'an Nijeriya ba su fayyace tsawon lokacin kasancewar sojojin Amurka ba, hukumomin Amurka sun nuna cewa an tsara tura sojojin ne a matsayin na wucin-gadi.

Rumbun Labarai
Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta soma bincike kan zargin kisan fararen-hula a kasuwar Jilli ta Yobe
ADC ta taya sabbin shugabannin jihohi murna, ta tsayar da ranar 12 ga Mayu don rantsar da su
Gwamnatin Nijeriya ta ba da umarnin soke fasfo ɗin mutanen da suka janye daga kasancewa ’yan ƙasar
Man fetur yana tsada sosai, amma mu gode wa Allah halin da muke ciki ya fi na wasu ƙasashe – Tinubu
An gano gawarwaki 61 bayan harin ta'addanci a jihar Neja ta Nijeriya
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda tare da ƙwace makamai a Jihar Filato
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce an kashe dakarunta a harin da Boko Haram ta kai hedkwatarsu a Borno
‘Gwarazan da ba za a iya mantawa da su ba’, Tinubu na juyayin kisan sojojin Nijeriya a harin Borno
Amurka ta bai wa jami'anta umarnin barin ofishin jakadancinta a Nijeriya saboda rashin tsaro a ƙasar
Aƙalla mutum 60 aka kashe a hare-hare daban-daban a arewa maso yammacin Nijeriya cikin mako guda
Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Nijeriya zai habaka a 2026
An mayar da 'yan Nijeriya 179 gida daga Libya
Babbar kotun Nijeriya ta ɗaure 'yanta'adda biyar
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda biyar, sun kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane a Filato
Matatar Dangote ta ƙara man da take turawa ƙasashen Afirka yayin da yaƙin Iran ya katse jigilar mai
An buƙaci Nijeriya ta gyara yadda ake bayar da labaran rikice-rikice
An kama mutum biyar kan harbin bindiga ba bisa ƙa’ida ba da 'ya kashe' yarinya Maiduguri a Nijeriya
Abin da ya sa Kano Pillars ta lallasa Bendel Insurance da ci 4-0 — Koci
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda yaran Ado Aleiro
‘Yanta’adda sun kai hari ofishin ‘yansanda a Borno, sun kashe jami’ai huɗu