Sojojin Rasha sun taimaka wajen daƙile wani hari a filin jirgin saman Diori Hamani da ke Yamai, babban birnin Jamhuriyar a makon jiya wanda ƙungiyar Daesh ta ɗauki nauyinsa, kamar yadda Moscow ta bayyana a ranar Litinin.
Gwamnatin Nijar ta bayyana kwanan baya cewa “abokan hulɗa ‘yan Rasha” sun taimaka wajen daƙile harin da ba kasafai ake samu ba a babban birnin ƙasar, lamarin da ya sa aka kashe mahara 20 tare da jikkata sojoji huɗu.
"An daƙile harin ta hanyar ƙoƙari na haɗin gwiwa na dakarun tsaron Rasha da ke Afirka da kuma rundunar sojin Nijar," kamar yadda ma’aikara harkokin wajen Rasha ta bayyana.
"Moscow ta yi Allah wadai da wannan hari na masu tsattsaura ra’ayi na baya bayan nan," in ji ta.
Nijar ta zargi Jamhuriyar Benin da Faransa da Ivory Coast da ɗaukar nauyin hari a filin jiragen sama, wanda ya ƙunshi wani sansanin sojin ƙasar.
Shugaba Abdourahamane Tiani ya ziyarci sansanin sojin Rasha domin bayyana "godiyarsa bisa wannan babban mataki na ƙwararru", in ji ma’aikatar.
Rasha ba ta cika tsokaci game da harkokin sojinta a yankin Sahel ba, inda Moscow take ƙara tasiri bayan an yi wasu jerin juye-juyen mulki na ƙin jinin Ƙasashen Yamma.
Yayin da take fuskantar wariya daga Yammacin Duniya bayan fara yaƙi da Ukraine, Moscow ta yi ƙoƙarin tsara sabuwar hulɗa a Afirka, inda take ƙara tasirinta a fagen siyasa da tattalin arziki da soji a ‘yan shekarun nan.
Baya ga Nijar, an ba da rahoton cewa an tura da dakarun Rasha ko kuma masu ba da horon soji zuwa Burkina Faso da Equatorial Guinea da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka (CAR) da kuma Libya.
Ɓangaren soji na ma’aikatar tsaron Rasha a Afirka ya karɓi ragama daga dakarun rundunar sojojin haya ta Wagner a faɗin nahiyar.
Moscow ta ce rundunar tana ba da gudunmawa wajen “ yaƙar ‘yanta’adda” da kuma “ƙarfafa zaman lafiyar yankin” Sahel.
Hukumomin Nijar sun shafe shekaru goma suna yaƙar ƙungiyar ta’addanci ta JNIM mai alaƙa da Al-Qaeda da ƙungiyar Daesh-Sahel a yammaci da kudu maso gabashin ƙasar.










