Shugaban rundunar sojin Nijar ya zargi Faransa, Benin da Côte d'Ivoire da laifin kai hari kan sansanin soja a filin jirgin saman kasa da kasa na Niamey, kuma ya gode wa sojoji da "abokan hulɗa na Rasha" saboda daƙile harin.
Wasu da ake zargin 'yanta'adda ne suka kai hari jim kadan bayan ƙarfe 12 na dare a ranar Alhamis, inda mazauna yankin suka ba da rahoton harbe-harbe da fashewar abubuwa har zuwa lokacin aka samu kwanciyar hankali kimanin awa daya bayan faruwar lamarin.
Nijar, wadda ta sha fama da tashin hankali na ta'addanci, na karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tiani tun bayan juyin mulkin da ya kifar da tsohon Shugaban Ƙasa Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.
Babu wata kungiyar 'yanta'adda da ta dauki alhakin kai harin zuwa yanzu.
An dawo da ayyukan tsaro kamar yadda aka saba a filin jirgin saman Diori Hamani, wanda ke da sansanin sojojin sama kuma yana da nisan kilomita 10 (mil shida) daga Fadar Shugaban Ƙasa.
Ma'aikatar tsaron Nijar ta ce an jikkata sojoji hudu kuma an kashe maharan 20, inda gidan talabijin na gwamnati ya ce wani dan kasar Faransa na cikin su.
Labari mai alaka: An kashe ’yanbindiga 20 a harin da aka kai sansanin sojojin sama a Nijar: Ma’aikatar Tsaro
An kama mutum 11, in ji ma’aikatar.
"Muna yaba wa dukkan jami'an tsaro... da kuma abokan hulɗa na Rasha waɗanda suka kare ɓangaren tsaronsu da ƙwarewa," in ji Tiani ta gidan rediyon gwamnati.
"Muna tunatar da masu tallafawa waɗannan mayakan, musamman Emmanuel Macron, Patrice Talon da Alassane Ouattara: mun ji sun yi ihu sosai; yanzu ya kamata su shirya su saurare mu."
Danganta tsakanin gwamnatin Nijar da tsohuwar kasar da ta yi mata mulkin mallaka ta yi tsami, kuma tana yawan zargin ta, da ma makaciyarta Benin da yunkurin rikita harkokin siyasar cikin gidanta, zargin da dukkan kasashen biyu suka musanta.
Ministan Tsaro Salifou Modi ya ce harin ya ɗauki "kimanin mintuna 30", kafin a "dauki matakin murkushe shi ta sama da ƙasa".
'Sojojin haya na Rasha'
Ibrahim Boubacar, shugaban wata ƙungiyar matasa da ke zaune kusa da filin jirgin sama, ya ce: "Mun fara jin harbe-harbe. Da farko, mun yi tunanin harbi ne kawai, sannan sai ya yi kama da na manyan bindigogi, da kuma rokoki.
"Mun gaya wa kanmu cewa da gaske harin ta'addanci ne."
Hotunan tauraron dan adam da AFP ta gani sun nuna wurare da alamun ƙonewar ƙasa kusa da titin jirgin saman.
Nijar na fama da tashin hankali daga 'yan ta'adda da ke da alaƙa da Al-Qaeda da Daesh, musamman a yammacin ƙasar kusa da babban birninta.
Ƙungiyar 'yan jarida ta Yammacin Afirka Wamaps, wacce ta ƙware kan batutuwan tsaro a yankin, ta yi magana game da "babban harin na ta'addanci da ya haɗa da jiragen sama marasa matuƙa, rokoki da 'yan ta'adda a kan babura".
.Ta ce nan da nan an yi amfani da garkuwar makamai masu linzami, wanda hakan ya sa aka "kassara mafi yawan maharan ko kuma suka gudu".
Wamaps ta ce "'sojojon haya na Rasha" sun shiga arangamar. A halin yanzu shafin watsa labarai na sojojin Rasha Rybar ya ce "akwai yiwuwar ƙwararrun sojojin Rasha sun taimaka wa sojojin gwamnati wajen dakile harin".
Bayan tabbatar da cewa sojojin Faransa da na Amurka sun fice daga yankinta, gwamnatin Nijar ta matsa kusa da sabbin abokan hulɗa, ciki har da Rasha.
Wuri mai muhimmanci
Filin jirgin saman wuri ne mai muhimmanci, wanda ke dauke hedikwatar rundunar haɗin gwiwa da Nijar, Burkina Faso, da Mali suka ƙirƙira don yaƙi da ƙungiyoyin 'yan ta'adda masu kai hare-hare a yankin.
Cibiyar jiragen sama kuma tana ɗauke da sansanin sojojin sama na Nijar da sansanin jiragen sama marasa matuki da aka gina kwanan nan. A cewar Wamaps, akwai sojojin Italiya kusan 300 a wajen.
Burkina Faso da Mali da Nijar sun haɗu don ƙirƙirar Kungiyar Kasashen Sahel (AES), kuma sun sanar da kafa rundunar sojoji mai dakaru 5,000 don ayyukan soji na haɗin gwiwa.













