Saif al-Islam Gaddafi: An kashe ɗan marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi

An kashe ɗan marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi a birnin Zintan da ke yammacin Libya, kamar yadda lauyansa Khaled al-Zaidi da mai ba shi shawarwari Abdullah Osman suka bayyana.

By
An kashe Saif al-Islam Gaddafi, ɗa ga marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi, a Libya, kamar yadda kafafan watsa labaran ƙasar suka ruwaito. / Reuters

An kashe ɗan marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi, Saif al-Islam Gaddafi, mai shekara 53, kamar yadda majiyoyin da ke kusa da iyalinsa suka bayyana, in ji lauyansa Khaled el-Zaydi da kuma kafofin watsa labaran Libya.

Mai ba shi shawarwari Abdullah Osman ya tabbatar da mutuwarsa ranar Talata.

Kafofin watsa labaran Libya sun ba da rahoton cewa kisan ya faru ne a gidansa kuma mutum huɗu da ba a san ko wane ne su ba suka aikata kisan, suna masu ƙarawa da cewa, an kashe kamarorin sa ido a gidan kafin a kai harin.

Ofishin babban lauyan Libya ya fara bincike game da kisan, in ji kafofin watsa labaran ƙasar.

Kawo yanzu dai bayanai game da kisan Saif al-Islam na da sarƙaƙiya kuma hukumomin Libya ba su fitar da bayani a hukumance da zai tabbatar da lamarin ba.

Ta shafinsa na Facebook, Moussa Ibrahim, wani tsohon mai magana da yawun Gaddafi, ya rubuta cewa: "Sun kashe shi cikin hai’inci yayin da yake son samar da haɗaɗɗiyar Libya mai ‘yancin kai da zai kare dukkan mutanenta …Sun shuka ƙiyayya da gaba."

Game da kisan gillan da aka yi wa Saif-al-Islam, Ibrahim ya ce: "Manufar ita ce ƙarin zubar da jini da raba Libya da kuma lalata dukkan shirin haɗin kan ƙasa, inda yake kare muradun baƙi a ƙasar."

Tun da aka kama shi bayan an yi juyin-juya-hali da ya hamɓarar da gwamnatin mahaifinsa a shekarar 2011, Saif-al-Islam yana zaune a birnin Zintan, da ke da nisan kilomita 136 kudu maso yammacin babban birnin ƙasar Tripoli, amma babu wanda ya san inda yake bayan an sake shi a shekarar 2017.