Lebanon ta saki Hannibal Gaddafi, ɗan tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi, bisa sharadin beli, bayan da ya shafe kusan shekaru goma yana ɗaure a kurkuku, in ji lauyansa.
"Mun bar wurin, yanzu ya samu yanci," in ji Laurent Bayon a ranar Litinin, awanni kaɗan bayan an biya kudin beli har dala 900,000.
Ana zargin Hannibal Gaddafi mai shekaru 49 da boye bayanai game da bacewar limamin Shi’a na Lebanon Mussa Sadr a Libya a 1978, amma ba a taba gurfanar da shi a kotu ba.
A lokacin batan Sadr, Hannibal yana da shekaru biyu.
"An biya jinginar ne da safiyar yau," in ji Lauya Bayon kamar yadda ya fada tun da fari a ranar Litinin. "A karshe Hannibal Gaddafi zai sami yanci. Wannan shi ne ƙarshen wani mafarki mai muni da ya ɗauki shekaru 10 a rayuwarsa."
A watan Oktoba, wani alkalin kotu ya umurci a saki Gaddafi idan an biya jinginar dala miliyan 11, wanda aka rage zuwa $900,000 makon da ya gabata bayan ƙorafin tawagar kare shari'a.
Wata majiya a bangaren shari'a a Lebanon ta tabbatar a ranar Litinin cewa an biya jinginar, kuma tawagar lauyoyinsa na kammala tsare-tsaren sakin sa.
Bayon ya ce wanda yake karewa zai bar Lebanon zuwa wani wuri 'na sirri', ya kuma ce yana da fasfo na Libya.
"An tsare Gaddafi ba tare da dalili ba a Lebanon har tsawon shekaru 10 ne saboda tsarin shari'ar kasar bai kasance mai 'yanci ba," in ji Bayon.
Ya ce sakin wanda yake karewar na nuna dawo da 'yancin shari'a ƙarƙashin gwamnati mai kawo sauyi ta Lebanon da aka kafa a watan Janairu.
Mussa Sadr — wanda ya kafa ƙungiyar Amal, wacce yanzu ta kasance abokiyar haɗin gwiwa ta Hezbollah — ya ɓata yayin ziyarar hukuma a Libya, tare da wani mai taimaka masa da kuma wani ɗan jarida.
Beirut ta dora laifin bacewar tasu a kan shugaba na Libya a lokacin, Muammar Gaddafi, wanda aka kawar da shi kuma aka kashe shi bayan gomman shekeru a tashin hankalin da aka yi a kasar a 2011.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi sanyi tun bayan bacewar wadannan mutane uku.
Hannibal, wanda ya auri Aline Skaf, wata mai tallan ayan kawa daga Lebanon, ya tsere zuwa Siriya bayan barkewar tashin hankali a 2011 a Libya.
An sace shi a Disamban 2015 inda wasu maza masu makamai suka kai shi Lebanon, inda hukumomi suka kwato shi daga hannun masu garkuwa sannan daga baya suka tsare shi.



















