Jami'an tsaro a Nijeriya sun kashe 'yanfashin daji da dama a Jihar Kogi
"An samu sakamako mai kyau a haɗin gwiwa tsakanin 'yansanda da sojoji wajen ci gaba da daƙile barazanar hare-haren 'yanfashin daji a Jihar Kogi," a cewar sanarwar 'yansanda.
Rundunar 'yansandan Jihar Kogi a arewa ta tsakiyar Nijeriya ta kawar da 'yanfashin daji da dama sannan ta wargaza hanyoyin sadarwarsu a yayin wani samame da ta ƙaddamar, ko da yake ba a bayyana takamaiman wurin da aka gudanar da aikin ba.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, mai magana da yawun rundunar, William Aya, ya ce an samu nasarar ce sakamakon wani aikin haɗin gwiwa da ya ƙunshi jami’an 'yansandan jihar da sojoji, tare da goyon bayan rundunar 'yansandan Nijeriya.
"An samu sakamako mai kyau a haɗin gwiwa tsakanin 'yansanda da sojoji wajen ci gaba da daƙile barazanar hare-haren 'yanfashin daji a Jihar Kogi," a cewar sanarwar 'yansanda.
"An fatattaki 'yanfashin daji, an wargaza hanyoyin sadarwarsu, sannan an kawar da wasu da dama," in ji sanarwar tana mai ƙari da cewa an gudanar da aikin ne cikin ƙwazo da jajircewa, bisa goyon bayan sassan rundunar 'yansandan Nijeriya ta hanyar kai hare-hare ta sama.
Rundunar ta buƙaci jama'a da su yi taka-tsantsan kana su kai rahoton duk wanda aka gani da raunukan harbin bindiga, ko wani mummunan rauni ko kuma wani abu da ake zargi ga ofishin 'yansanda mafi kusa.
Kazalika sanarwar ta yi kira ga mazauna jihar da su goyi bayan ayyukan da ake yi ta hanyar samar da ingantattun bayanai game da masu aikata laifuka a cikin unguwanninsu.
'Yanfashin dajin sun ƙara tsananta ayyukan laifuka a sassa da dama na jihar Kogi a cikin 'yan watannin nan.
A tsakanin watan Oktoba da Disamba na 2025, an kai hare-hare kan coci-coci biyu, lamarin da ya sa hukumomi a jihar suka sanya dokar hana gudanar da duk wani taron addini har baba-ta-gani.