'Yansandan Nijeriya sun kashe ɓarayin daji tare da kama mai safarar makamai a Kaduna
Rundunar 'yansandan ta kuma kama waɗanda ake zargi da kasancewa infoma da masu safarar miyagun ƙwayoyin da ke alaƙa da masu aikata laifuka.
Rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen Jihar Kaduna ta ce ta yi nasarar kashe ɓarayin daji da dama yayin wani aikin kakkaɓe ‘yanbindiga bayan samun bayanan sirri a Kajuru da Tafa da Igabi da kuma Kauru a cikin watan Fabrairun shekarar 2026.
Da yake jawabi ga manema labarai a Kaduna, kwamishinan ‘yansandan jihar, Rabiu Muhammad, ya ce ayyukan sun mayar da hankali ne kan maɓoyun ɓarayin dajin da aka gano.
An lalata wasu dabobi a lokacin musayar wuta, inda aka kashe wasu ‘yanbindiga, yayin da saura suka tsere da raunuka.
‘Yansanda sun kuma kama wasu da ake zargi da kasancewa infoma da masu safarar miyagun ƙwayoyi da ke da alaƙa da ƙungiyoyin masu laifuka, in ji shi.
Muhammad ya bayyana cewa an kama gawurtattun ‘yanbindiga da wasu mutum biyar da ake zargi da kasancewa masu safarar makamai a lokacin samamen.
Kayayyakin da aka ƙwace sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47 guda uku, da bindigogi 21, da wata ƙaramar bindiga mai jigida da ƙananan bindigogi biyu da kuma ƙananan bindigogi huɗu da aka ƙera a gida da kuma miyagun ƙayoyi masu yawa.
Daga farko dai ranar 17 ga watan Fabrairu jami’an ‘yansanda da ke aiki bisa bayanan sirri sun kama mutum uku — Peter Pama da Saleh Monday da kuma Sunday Makama — a Kasuwan Magani game da zargin cinikin makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Rahotannisun ce waɗanda ake zargin an same su ne da wata bindiga ƙirar AK-47 da aka yi a gida da kuma bindiga ƙirar pump-action.
A wani samame na daban da aka kai ranar 20 ga watan Fabrairu, jami’an tsaro daga ɓangaren yaƙi da garkuwa da mutane sun kama Adamu Aminu na garin Jaji a ƙaramar hukumar Igabi .
Wanda ake zargin an same shi ne da bindigogi shida ƙirar AK-47 da aka yi a gida da ƙananan bindgogi da aka yi a gida, in ji rundunar ‘yansandan.
An kama wani da ake zargi, Abubakar Hassan, na Unguwar Rogo a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, bisa alaƙarsa da batun.
Rundunar ‘yansandan ƙasar ta ce bincike na wucin-gadi ya nuna cewa waɗanda ake zargin suna da hannu a ƙera makamai da kuma sayarwa ba bisa doka ba, lamarin da rundunar ta ce yana ruta wutar aikata laifuka a ciki da wajen jihar Kaduna.
Rundunar ta ƙara da cewa ana kan gudanar da bincike domin kakkaɓe harkar safarar makaman da kuma ƙwace su.