'Yanbindiga sun raba fiye da mutum 300,00 da gidajensu a jihar Neja – Gwamna Bago
Waɗannan hare-haren sun katse hanyoyin samun mutane tare da tilasta wa mutane barin gidajensu da kuma ƙarfafa rashin tsaro a yankunan karkara.
Gwamnan Jihar Neja a arewacin Nijeriya, Umaru Mohammed Bago, ya bayyana cewa fiye da mutum 300,000 ne hare-haren ‘yanbindiga babu ƙaƙƙautawa suka raba da gidajensu a ƙananan hukumomi 10 na jihar.
Jihar Neja tana ɗaya daga cikin jihohin da hare-haren ‘yanbindiga suka fi ƙamari inda ƙungiyoyin ‘yanbindiga suke yawan kai hare-hare kan al’umomi masu rauni kuma suke kashe tare da garkuwa da mazauna wuraren ciki har da ‘yan makaranta.
Waɗannan hare-haren sun katse hanyoyin samun mutane da tilasta wa mutane barin gidajensu da kuma ƙarfafa rashin tsaro a yankunan karkara.
Saboda haka, iyalai da yawa a halin yanzu suna rayuwa ne cikin tsoro na dindindin. Mutane sun bar gonaki saboda tsoron tashin hankali yayin da iyaye suke jin tsoron tura ‘ya’yansu makaranta.
Hare-haren babu ƙaƙƙautawa ba harkar noma kawai suka shafa ba, sun dagula harkar jinƙai a jihar.
Da yake magana da ‘yanjarida ranar Asabar a Minna, babbin birnin jihar bayan ya karɓi tallafin jinƙai daga gwamnatin tarayya, Gwamna Bago ya bayyana cewa ana ƙoƙarin tattara cikakkun bayanai game da mutanen da aka raba da muhallansu saboda ana ci gaba da kai hare-hare kan ƙananan hukumomi.
“A halin yanzu, ƙiyasi kawai za mu iya bayarwa. Aƙalla muna da mutane fiye da 300,000 da aka kora daga digajensu a ƙananan hukumomi fiye da 10 da ke fama da rashin tsaro,” in ji shi.
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya cikin al’ummonin da ke fama da rashin tsaro.
Ya bayyana fatansa cewa matakan tsaron da ake ɗauka za su sa waɗanda aka raba da muhllansu su koma gida da kuma koma rayuwa yadda suka saba.