| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Jihar Neja ta karɓi ɗalibai 100 na St. Mary’s Catholic School da aka ceto
Ɗaliban na makarantar St. Mary’s Catholic School sun isa gidan gwamnatin Jihar Neja ne a cikin motocin bas da misalin ƙarfe 5:20 na yamma sannan Gwamna Bago da wasu jami'an gwamnatinsa suka tarbe su.
Gwamnatin Jihar Neja ta karɓi ɗalibai 100 na St. Mary’s Catholic School da aka ceto
'Yanbindiga sun kai hari a makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri a Jihar Neja ne watan Nuwamba inda suka sace ɗalibai 303 da malamai 12. / AP
9 Disamba 2025

Gwamnan Jihar Neja Umar Bago ranar Litinin ya jagoranci manyan jami’an gwamnati da ‘yansiyasa wajen tarbar ɗalibai 100 na makarantar St. Mary Catholic ta ƙauyen Papiri da ke ƙaramar hukumar Agwara.

Wakilin Nuhu Ribadu, mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan sha’anin tsaro ne ya miƙa wa Gwamna Bago ɗaliban.

A jawabinsa ya yi miƙa ɗaliban, Wing Commander Abdullahi Dare ya ce ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro tare da haɗin gwiwar dakarun sojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro ne suka kuɓutar da ɗaliban.

A nasa jawabin, Gwamna Bago ya gode wa shugaban Nijeriya Bola Tinubu da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro da dukkan jami’an tsaron ƙasar da ma masu ruwa da tsaki kan rawar da suka taka wajen kuɓutar da ɗalibai 100.

Masu AlakaTRT Afrika - Gwamnatin Nijeriya ta karɓo ɗalibai 100 da aka sace daga St. Mary’s Catholic School a Jihar Neja

Tun da farko ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya, CAN, ta hannun shugabanta reshen Jihar Neja, Bishop Bulus Yohanna, ta ce ba ta samu bayanai a hukumance ba kan kuɓutar da ɗaliban.

A ranar 21 ga watan Nuwamban 2025, wasu ‘yanbindiga a kan babura suka kai hari a St. Mary’s Catholic School inda suka sace mutum 315 —ɗalibai 303 da malamai 12.

Jami’an tsaro da mafarauta sun fantsama cikin dajin yankin inda suka yi ta neman mutanen da aka sace.

Daga bisani, hukumomin makarantar sun ce ɗalibai aƙalla 50 sun tsere daga masu garkuwa da mutanen inda suka koma wurin iyayensu.