| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yansanda sun tabbatar da mutuwar mutum 33 a harin Kebbi
Hukumomin 'yansanda sun bayyana rashin jindaɗin game da rasa raukan yayin da suka miƙa saƙon ta'aziyyarsu ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
'Yansanda sun tabbatar da mutuwar mutum 33 a harin Kebbi
Rundunar 'yansandan Nijeriya ta jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu / Others
20 Fabrairu 2026

Rundunar ‘yansandan jihar Kebbi ta tabbatar da cewa an kashe mutum 33 a wani harin da aka kai gundumar Bui a ƙaramar hukumar Arewa bayan an yi wani fashin shanu da makami.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Kebbi, Bashir Usman ne ye bayyana wannan a wata sanarwa.

“A matsayin martani, rundunar tare da sojoji da sauran hukumomin tsaro, ta tura ƙarin ma’aikata da kayayyakin aiki zuwa wuraren da lamarin ya faru. A halin yanzu ana ci gaba da sintiri na tabbatar da iko a wurin domin tabbatar da zaman lafiya,” in ji sanarwar Usman.

Hukumomin ‘yansanda sun bayyana matuƙar rashin jin daɗinsu game da rasa rayukan kuma sun miƙa saƙon ta’aziyya ga al’ummar ƙaramar hukumar Arewa Community.

Sanarwar ta ƙara da cewa bincike na farko-farko ya nuna cewa wasu da ake ganin mayaƙan Lakurawa ne suka shiga gundumar Bui domin fashin shanu.

An yi imanin cewa maharan sun tsallako wurin ne daga ƙaramar hukumar Gudu a jihar Sokoto mai maƙwabtaka.

Labari mai alaƙa: Mutane da dama sun rasa rayukansu a hare-haren Lakurawa a Jihar Kebbi a Nijeriya

Rahotanni sun ce mazauna wurare kamar Mamunu da Awasaka da Tungan Tsoho da Makangara da Kanzo da Gorun Naidal da kuma Dan Mai Ago sun haɗa kai domin tunkarar maharar lamarin da ya kai ga rangama na makamai da ƙungiyar ‘yan bindigar.

Rundunar ‘yansandan jihar ta jaddada cewa duk abinda ya shafi ƙungiyoyin masu aikata laifuka na buƙatar tsara matakin tsaro na hadin gwiwa.

Hukumomi sun yi kira ga mazanuna wuraren su ba da rahoton duk wani abin da ba su yarda da shi ba ta hnayoyin sadarwa na tsaro maimakon tunkararsu kai tsaye, suna masu gargadin cewa irin wannan arangamar na da matuƙar haɗari.

Rumbun Labarai
Nijeriya na neman tallafin IMF da Bankin Duniya don rage tasirin yakin Iran kan tattalin arziki
Me ya sa hare-hare ke karu wa a Nijeriya duk da wanzuwar dakarun Amurka?
Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta soma bincike kan zargin kisan fararen-hula a kasuwar Jilli ta Yobe
ADC ta taya sabbin shugabannin jihohi murna, ta tsayar da ranar 12 ga Mayu don rantsar da su
Gwamnatin Nijeriya ta ba da umarnin soke fasfo ɗin mutanen da suka janye daga kasancewa ’yan ƙasar
Man fetur yana tsada sosai, amma mu gode wa Allah halin da muke ciki ya fi na wasu ƙasashe – Tinubu
An gano gawarwaki 61 bayan harin ta'addanci a jihar Neja ta Nijeriya
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda tare da ƙwace makamai a Jihar Filato
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce an kashe dakarunta a harin da Boko Haram ta kai hedkwatarsu a Borno
‘Gwarazan da ba za a iya mantawa da su ba’, Tinubu na juyayin kisan sojojin Nijeriya a harin Borno
Amurka ta bai wa jami'anta umarnin barin ofishin jakadancinta a Nijeriya saboda rashin tsaro a ƙasar
Aƙalla mutum 60 aka kashe a hare-hare daban-daban a arewa maso yammacin Nijeriya cikin mako guda
Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Nijeriya zai habaka a 2026
An mayar da 'yan Nijeriya 179 gida daga Libya
Babbar kotun Nijeriya ta ɗaure 'yanta'adda biyar
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda biyar, sun kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane a Filato
Matatar Dangote ta ƙara man da take turawa ƙasashen Afirka yayin da yaƙin Iran ya katse jigilar mai
An buƙaci Nijeriya ta gyara yadda ake bayar da labaran rikice-rikice
An kama mutum biyar kan harbin bindiga ba bisa ƙa’ida ba da 'ya kashe' yarinya Maiduguri a Nijeriya
Abin da ya sa Kano Pillars ta lallasa Bendel Insurance da ci 4-0 — Koci