| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
‘Yansandan Nijeriya sun dakile harin ‘yanbindiga a Sokoto
A cewar sanarwar, an gudanar da aikin ne bayan samun kiran gaggawa da ke nuna cewa ɗimbin ’yanbindiga masu ɗauke da muggan makamai sun mamaye ƙauyen Daraye.
‘Yansandan Nijeriya sun dakile harin ‘yanbindiga a Sokoto
Jami’an tsaron sun yi musayar wuta mai ƙarfi da maharan / Others

Rundunar ’yansandan Nijeriya reshen Jihar Sokoto ta daƙile wani hari da ’yanbindiga suka kai ƙauyen Daraye da ke Ƙaramar Hukumar Wamakko, inda ta kashe wani da ake zargin ɗanbindiga ne tare da kwato bindigar AK-47 da harsasai.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya fitar, inda ya ce wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na ci gaba da yaƙi da ’yanbindiga da sauran barazanar tsaro a faɗin jihar.

A cewar sanarwar, an gudanar da aikin ne bayan samun kiran gaggawa da ke nuna cewa ɗimbin ’yanbindiga masu ɗauke da muggan makamai sun mamaye ƙauyen Daraye.

Masu AlakaTRT Afrika - Yadda matsalar tsaron Nijeriya ke ƙara barazana ga wadatar abinci

Bayan samun bayanin, jami’an sashen yaƙi da masu garkuwa da mutane, da Daƙile Laifuka a Ƙauyuka (VCRU), tare da sauran ƙungiyoyi na musamman, sun garzaya domin taimaka wa jami’an da ke Hedikwatar ’Yansandan Wamakko.

Jami’an tsaron sun yi musayar wuta mai ƙarfi da maharan, lamarin da ya tilasta wa ’yanbindigar tserewa zuwa cikin daji da raunukan harbin bindiga daban-daban.

A yayin ci gaba da sintiri da bincike a yankin, an kashe wani da ake zargin ɗanbindiga ne, yayin da aka ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya da kuma ma’ajiyar harsasai ɗauke da harsasai masu rai guda 28 na nau’in 7.62mm.

Sanarwar ta ƙara da cewa an ƙara yawan sintirin tabbatar da zaman lafiya a yankin, yayin da aka sanya ofisoshin ’yansanda na maƙwabtan yankuna cikin shirin ko-ta-kwana domin cafke waɗanda suka tsere, musamman idan suka nemi kulawar lafiya saboda raunukan da suka samu.