| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda yaran Ado Aleiro
Rahotanni sun ce jami'an tsaron sun yi nasarar ne yayin wani bata-kashi da suka yi da 'yan ta'addan a ƙaramar hukumar tsafe ta jihar Zamfara a arewa maso yammacin Nijeriya.
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda yaran Ado Aleiro
Jami'an tsraon sun yi nasarar ne bayan an bata-kashi tsakaninsu da 'yanta'addan / AFP
4 awanni baya

Rahotanni daga Nijeriya na cewa dakarun ƙasar sun yi nasarar kashe gomman ‘yanta’adda yaran ƙasurgumin ɗanbindiga Ado Aleiro a wata arangama da suka yi a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin ƙasar.

Gidan talbijin na Channels TV a Nijeriya ya ambato majiyoyin tsaro na cewa an fara arangamar ne ranar Asabar da yamma lokacin da ɓarayin dajin suka kai wa ‘yan sa-kai hari a ƙauyen Kunchin Kalgo.

Daga nan sai aka haɗa wata tawagar jami’an tsaro domin kai wa ‘yan sa-kan ɗauki lamarin da ya janyo bata-kashin da aka yi tsakanin ‘yanta’addan da jami’an tsaro.

Channels TV ya ambato wani jami’in tsaro da ke cikin waɗanda suka kai ɗaukin yana cewa, “Mun rinjaye su kuma mun bi su har cikin dajin Munhaye, inda aka kashe ɓarayin daji fiye da 30.”

Daga cikin waɗanda rahotanni ke cewa an kashe akwai Kachalla Iliya Sarki, wanda aka ce ɗa ne ga ƙasurgumin shugaban ɓarayin daji Ado Aleiro, tare da wani babban ƙasurgumin ɓarawon daji mai suna Dogo Bete.

Masu AlakaTRT Afrika - ‘Yanta’adda sun kai hari ofishin ‘yansanda a Borno, sun kashe jami’ai huɗu

Mai magana da yawun dakarun Operation Fansan Yamma mai yaƙi da ta’addanci a arewa maso yammacin ƙasar, David Adewusi, ya ce duk da cewa an kashe wasu ‘yanta’adda, ba za a iya tantance adadin ‘yanta’addan da aka kashe ba domin ana ci gaba da aikin kakkabe ragowan ‘yanta’addan da ke wurin.

“Haka ne, mun yi arangama jiya da ‘yanta’adda, kuma an kashe gommai daga cikinsu. Ba za mu iya tabbatar da adadin su ba a wannna lokacin, amma an yi arangama,” in ji shi.

Sai dai kuma rahotanni sun ce an kashe ‘yansakai fiye da 10 a arangamar.

Sojin Nijeriya sun kuɓutar da mutane bayan hari a coci a Kaduna

A wani labarai makamancin hakan, rundunar sojin Nijeriya ta bayyana ranar Lahadi cewa ta ceto fararen-hula 31 da aka yi garkuwa da su yayin wani hari kan wani coci a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin ƙasar, yayin da aka samu gawarwakin mutum biyar a wurin.

Rundunar sojin ta ce an kai harin ne yayin ibada na bikin Easter a wani coci da ke ƙauyen Ariko na ƙaramar hukumar Kachia da ke jihar.

Rundunar ta ƙara da cewa dakaru na bin maharan.

Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen jihar Kaduna, Caleb Maaji, ya ce coci biyu aka kai wa hari a ƙauyen Ariko ranar Lahadi. Ya ce an kashe mutum bakwai kuma an yi garkuwa da mutane da ba a san adadinsu ba .

"Har yanzu dai ana bincike," kamar yadda Maaji ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters.

Arewa maso yammacin Nijeriya ta shafe shekaru tana fama da tashe-tashen hankula ciki har da garkuwa da mutane da yawa a lokaci ɗaya domin neman kuɗin fansa da kai samame kan ƙauyuka inda ƙungiyoyin ‘yanbindiga ke aika-aika a cikin wuraren ɓuya a daji mai faɗi a fadin yankin.