Za a yi jana’izar ministan tsaron Mali, wanda aka kashe a wani harin da aka kai gidansa, ranar Alhamis, in ji rundunar sojin ƙasar.
An kashe Sadio Camara ne a gidansa a Kati, wani gari na soji kusa da babban birnin ƙasar, Bamako, bayan zazzafar musayar wuta a ƙarshen mako, wadda aka yi tsakanin soji da ‘yan a-ware a ƙarƙashin jagorancin Abzinawa da ‘yanta’adda.
Shugaba Assimi Goita zai halarci jana’izar Camara, wanda za a yi da misalin ƙarfe 10:00 na safe agogaon ƙasar (ƙarfe 10:00 kenan agogon GMT) a filin faretin sojoji injiniyoyi kuma zai haɗa da fareti a gaban gawar, in ji wata takarda da babban hafsan sojin ƙasar ya fitar.
Ana tsammanin ƙarfafa matakan tsaro a wurin.
Camara mai shekara 47 ya rasu ne a lokacin da wani "bam na mota da wani ɗan ƙunar- baƙin-wake ya tuƙa" ta afka wa gidansa, in ji gwamnatin Mali.
A wani jawabin da ya yi ga ƙasar ranar Talata da yamma, Goita ya yaba wa "jarumin hafsa" wanda "rasuwarsa ta kasance babban rashi" ga Mali.
Gwamnatin ta ayyana kwanaki biyu na zaman makoki bayan rasuwar Camara.









