Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya isa Aljeriya ranar Lahadi a wata ziyara ta aiki, inda ya tattauna da Shugaba Abdelmadjid Tebboune, a wani yunƙuri da ake ganin ya nuna ƙarshen fiye da watanni 10 na rashin jituwa tsakanin ƙasashen biyu.
Fadar shugaban ƙasar Aljeriya ta bayyana a cikin wata gajeruwar sanarwa a shafin Facebook cewa Tebboune ya karɓi Tiani, wanda ke jagorantar wata babbar tawaga, ba tare da ba da ƙarin bayani ba.
Gidan talbijin na ƙasar ya ba da rahoton cewa Tebboune ya yi maraba da takwaransa na Nijar a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Houari Boumediene a Algiers, yana mai bayyana ziyarar a matsayin wata aba da ke nuna “zurfin alaƙa ta tarihi” da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Bidiyon da aka nuna kan talbijin na ƙasa ya nuna wani bikin maraba da shugaban ƙasar, ciki har da saka taken ƙasashen biyu da kuma ƙaddamar da faretin ban-girma.
Manyan jami’an Aljeriya sun halarci bikin, ciki har da kakakin majalisar dokoki Azzouz Nasri da Hafsan soji Janar Said Chanegriha da ministan harkokin waje Ahmed Attaf da kuma ministan ma’adinai Mohamed Arkab, in ji talbijin na ƙasar.
Daga baya Tebboune da Tiani sun yi tattaunawa a ɓangare mai alfarma na filin jiragen saman tare da mamboin tawagogin biyun . Ba a ba da bayanai game da ttaunawar ba dai ko kuma tsawon lokacin ziyarar nan take.
Kafofin watsa labaran ƙasar da masu sharhi kan lamuran yau da kullum dai sun ce irin tarbar da aka yi da kum attaunawar da aka yi da manyan jami’ai sun nuna yadda ake kawo ƙarshen rashin jituwar da ta sa dangataka ta yi tsami na sama da watanni 10 .
Ranar Alhamis , Aljeriya ta yi shelar komawar Ahmed Saadi, jakadanta a Nijar, bayan ta yi ramuwar gayya wajen rage alaƙarta ta diflomasiyya tun watan Afrilun da ya gabata. Matakin ya biyo bayan komawar aikin jakadan Nijar a a Aljeriya, Aminou Malam Manzo, ranar Alhamis.
Sansatawa
Ce-ce-ku-cen na diflomasiyya ya soma ne a watan Afriulun da ya gabata, a lokacin da Nijar da Burkina Faso da Mali, mambobin ƙawancen ƙasashen Sahel na AES suka yi wa jakadunsu kiranye daga Aljeriya bayan Mali ta zargi Algiers da kakkaɓo ɗaya daga cikin jiragenta maras matuƙa.
Aljeriya ta bayyana a wancan lokacin cewa jirgin ya keta ‘yancin sararin samaniyarta a wata tafiya ta farmaƙi, a karo na uku.
Aljeriya ta mayar da martani ta hanyar yi wa jakadunta kiranye daga ƙasashen uku. Daga baya ta ce matakin Nijar ya samo asali ne daga kasancewarta mamba na ƙungiyar ƙasashen Sahel maimakon rikici tsakanin ƙsashen biyu.
A ƙarshen shekarar da ta gabata ne dai rashin jituwar ta fara raguwa.
A watan Nuwamba, shugaban Nijar ya tura wa Tebboune saƙo game da ranar tunawa da juyin-juya-halin Aljeriya.
A watan Janairu, ministan makamashin Aljeriya Mohamed Arkab ya ziyarci Nijar domin sake nazari kan ayyukan haɗaka na mai, wani babban jami’in Aljeriya na farko da ya ziyarci ƙasar tun bayan rage alaƙar diflomasiyyar.
Aljeriya da Nijar suna da kan iyaka ɗaya da ya kai kilomita 950 kuma suna haɗa kai kan muhimman ayyuka na yanki, ciki har da har da babban titin hamadar Sahara da kuma wani shirin samar da bututun gas da zai kai iskar gas ɗin Nijeriya zuwa Turai ta Nijar da Aljeriya. Wani babban aiki ne da zai iya ba da damar tura kubik mita na isgar gas biliyan 30 a ko wace shekara.














