| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Adadin waɗanda suka kamu da Ebola a Jamhuriyar Kongo ya haura 5,000
Adadin waɗanda suka mutu sakamakon Ebola ya kai 2,378 a daidai lokacin da ake fama da ƙarancin kayan aikin kiwon lafiya, turjiya daga wasu al'ummomi da rashin zaman lafiya waɗanda duka suke kawo cikas ga yaƙi da cutar.
Adadin waɗanda suka kamu da Ebola a Jamhuriyar Kongo ya haura 5,000
Cutar ta ƙara yaɗuwa tun bayan da aka ayyana ɓullar annobar a ranar 15 ga Mayu / AP

Adadin masu ɗauke da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya haura 5,000, kamar yadda bayanan gwamnati suka nuna a daren Talata, yayin da jami’an kiwon lafiya ke gargaɗin cewa ƙoƙarin daƙile cutar na fuskantar matsala wajen hana yaɗuwar wannan mummunar cuta.

Annobar Ebola ta 17 da ta ɓarke a ƙasar ta zama mafi girma a tarihin ƙasar ta fuskar yawan masu kamuwa da cutar a ƙarshen watan Yuli, yayin da adadin waɗanda suka mutu ya kai 2,378 a ƙarshen makon da ya gabata, a cewar cibiyar kula da lafiyar jama’a.

Masu AlakaTRT Afrika - Mutane fiye da 4,000 ne suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo - Gwamnati

Cibiyar ta yi rajistar mutane 5,021 da suka kamu da cutar a sabon rahoton halin da ake ciki, lamarin da ya sanya wannan annobar ta zama ta biyu mafi muni a duniya ta fuskar yawan masu kamuwa da cutar da kuma mace-mace, bayan annobar Ebola da ta auku a Yammacin Afirka tsakanin 2014 zuwa 2016.

Annobar ta samo asali ne daga nau’in Ebola mai suna Bundibugyo, wanda har yanzu ba a samu allurar rigakafi ko maganin da aka amince da shi a hukumance domin yakar sa ba.

Cutar ta ƙara yaɗuwa tun bayan da aka ayyana ɓullar annobar a ranar 15 ga Mayu, yayin da ƙarancin kayan aikin kiwon lafiya, turjiya daga wasu al’umma, rashin zaman lafiya da kuma zanga-zangar ma’aikatan da ke aikin yaƙi da cutar ke kawo cikas ga ƙoƙarin gano masu ɗauke da cutar da kuma dakile yaɗuwarta.