Trump na son ƙwace man Iran, ya sa ido a Tsibirin Kharg yayin da dakarun Amurka ke son shiga— rahoto
Shugaban Amurka ya ce abin da ya fi so shi ne ya "karɓe iko da man" da ke Iran, yana mai nuna cewa Washington za ta iya ƙwace muhimmiyar cibiyar fitar da kayayyaki ta Tsibirin Kharg.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce babban burinsa shi ne ya "karɓe iko da man" da ke Iran kuma ya nuna cewa Washington za ta iya ƙwace Tsibirin Kharg, wata muhimmiyar cibiyar fitar da kayayyaki, yayin da Amurka ta aika ƙarin dakarunta a Gabas Ta Tsakiya, in ji wani rahoton da jaridar Financial Times ta wallafa.
"Idan zan gaya maka gaskiya, abin da na fi so shi ne na karɓe iko da man da ke Iran," kamar yadda ya faɗa a cikin wata zantawa da jaridar Financial Times, yana mai kwatanta salon abin da yake so da yadda ya yi a Venezuela, inda Amurka take son ta riƙa juya akalar fannin man ƙasar "har abada."
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da farashin mai ya ƙaru da abin da ya zarce kashi 50 cikin 100 a cikin wata ɗaya, inda farashin ɗanyen mai nau’in Brent ya haura $116 kan ko wace ganga sakamakon yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a Iran.
"Ta yiwu mu ƙwace Tsibirin Kharg, ta yiwu ba za mu ƙwace ba. Muna da zaɓi da yawa," a cewar Trump, yana mai ƙarawa da cewa irin wannan matakin "zai kuma nuna cewa dole mu kasance a ƙasar na tsawon lokaci."
"Ba na tunanin suna da wata kariya. Za mu iya ƙwacewa cikin sauƙi," in ji shi .
Sojin Amurka a Gabas Ta Tsakiya
Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon ta ba da umarnin tura sojoji 10,000 da aka horas don yaƙi ta ƙasa, inda tuni kimanin 3,500 suka fara isa yankin, ciki har da kimanin sojin ruwa masu iya yaƙi a ƙasa guda 2,200, waɗanda aka fi sani da Marines, yayin da ƙarin dakaru ke tafe.
Jami’ai sun yi gargaɗin cewa kai hari kan Tsibirin Kharg zai iya ƙara barazana ga dakarun Amurka da kuma tsawaita yaƙin.
Abubuwan da suka faru kwanan nan sun haɗa da wani hari a kan wani sansanin sojin sama a Saudiyya wanda ya yi sanadin jikkata dakarun Amurka 12 da kuma lalata jirgin leƙen asirin da ƙimarsa ta kai dala miliyan 270 tare da hare-haren makamai masu linzami da dakarun Houthi na Yemen suka harba zuwa Isra’ila.
Duk da taɓarɓarewar lamura, Trump ya ce tattaunawa a kaikaice da Iran ta hanyar “masu shiga tsakani” ‘yan Pakistan na ci gaba, yana mai ƙarawa da cewa: "Za a iya cim ma yarjejeniya cikin sauri."
Ya kuma ce Iran ta ƙyale tankokin mai masu tutar Pakistan 20 sun wuce ta Mashigar ruwan Hormuz, yana mai cewa, "Sun ba mu 10. Yanzu za su ba mu 20."
Taɓarɓarewar lamura a yankin na ci gaba tun lokacin da Isra’ila da Amurka suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran ranar 28 ga watan Fabrairu, inda suka kashe fiye da mutum 1,340 kawo yanzu, ciki har da jagoran addinin ƙasar Ali Khamenei.
Iran ta rama da hare-haren jirage mara matuƙa da na makamai masu linzami kan Isra’ila da Jordan da Iraƙi da ƙasashen Labarawa da ke gaɓar teku da ke da kayayyakin sojin Amurka, lamarin da ya haddasa mace-mace da lalata ababen more rayuwa tare da dagula lissafin kasuwannin duniya da harkar sufurin sama ta duniya.