Ƙungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmai (OIC) ta yi Allah wadai da "munanan" hare-haren da ‘yan Houthi na Yemen suka kai birnin Makkah mai tsarki da kuma yankin Madinah.
A wata sanarwa da Babban Sakatariyar ƙungiyar ta fitar a hukumance kana ta wallafa a shafinta na X, OIC ta yi tir da harin da kuma ci gaba da kai hare-hare mayaƙan Houthi a ƙasar Saudiyya.
"Babban Sakatariyar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) na yin Allah-wadai da munanan hare-haren da kungiyar Houthi ta kai kan birnin Makka da yankin Madinah, tare da ci gaba da kai hare-hare kan Masarautar Saudiyya," in ji sanarwar.
Hare-hare a wurare masu tsarki
Kungiyar ta jaddada cewa irin waɗannan hare-hare suna haifar da fargaba da tsoro ga fararen-hula tare da take darajar hakkokin wurare masu tsarki da masallatai, da kuma tayar da hankulan musulmai a duk faɗin duniya.

Babban Sakatariyar ta tabbatar da cewa ayyukan da ake aikatawa kan wurare masu tsarki, da wuraren ibada, da kayayyakin more rayuwa na fararen-hula "sun zama ta'addanci da ya saɓa wa ɗabi'un Musulunci da ƙa'idoji da manufofi, da kuma dokokin ƙasa da ƙasa."
Ta jaddada cewa duk wani nau’in hari kan wurare masu tsarki na wakiltar "laifi da ba za a iya amincewa da shi ko haƙuri da shi ba, wanda ke buƙatar ɗaukar mataki na hana masu aikata shi da kuma daƙile duk wanda ya yi gangancin taɓa waɗannan wurare."
Ƙungiyar ta kuma bayyana cikakken goyonta ga Saudiyya da kuma dukkan matakan da Riyadh ta dauka don dakile hare-haren da kare tsaron kasa da ikon mallakar ƙasa, tare da kiyaye darajar wurare masu tsarki a faɗin ƙasar.
Sanarwar ta biyo bayan ƙungiyar ƙawancen ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta ya bayyana cewa tsarin tsaron sararin samaniyar Saudiyya ya daƙile tare da lalata wani jirgin sama maras matuƙi da 'yan Houthi suka harba kusa da Makka a ranar Talata.
Mai magana da yawun ƙungiyar ƙawancen, Turki al-Malki, ya ce an daƙile jirgin ne da misalin karfe 6:50 na yamma agogon yankin kafin ya shiga sararin samaniyar da aka haramta shiga, inda tarkacen jirgin ya faɗi a kudancin birnin Makka mai tsarki.
Al-Malki ya bayyana lamarin a matsayin karo na biyu da 'yan Houthi suka yi yunƙurin kai hari Makka, yana mai nuni kan wani hari na makami mai linzami da aka harba birnin a ranar 27 ga watan Yulin 2017.


















