Yoweri Museveni ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasar Uganda
Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar Alhamis bayan hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar.
Shugaban Uganda, Yoweri Museveni, ya lashe zaɓen shugaban ƙasar a ranar Asabar domin fara wa'adi na bakwai bayan wani zabe da aka yi mai cike da ce-ce-ku-ce.
Hukumar zaɓen ta ce Museveni, mai shekaru 81, ya samu kashi 71.65 na kuri'u a zaben ranar Alhamis.
Jam'iyyarsa mai mulki ta National Resistance Movement (NRM), na kan gaba a kujerun ‘yan majalisa kamar yadda sakamakon wucin-gadi ya nuna.
Wannan nasara ta ba shi damar tsawaita mulkinsa na kimanin shekaru 40 a kasar gabashin Afirka.
Ya doke Bobi Wine, mai shekaru 43, tsohon mawaki da ya koma ɗan siyasa, wanda ya samu kashi 24.72% inda a ranar Asabar ya ce ya ɓoye bayan rundunar tsaro ta kai hari gidansa.
Abokin hamayya a gudu
Ya bayyana “cikakken kin amincewa da sakamakon bogi' kuma ya ce yana gudu bayan farmakin gidansa a daren Jumma'a.
“Ina so in tabbatar da cewa na samu tserewa daga hannunsu,” kamar yadda Wine ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar. “A halin yanzu, ban kasance a gida ba, duk da cewa matata da wasu 'yan uwa an yi musu daurin-talala a gida.”
“Na san waɗannan masu laifin na nemana a ko'ina kuma ina ƙoƙarin yin iya bakin ƙoƙarina don samun tsaro,” in ji shi.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa jami'an 'yan sanda sun yi yawa a kewaye da babban birnin Kampala.
Yan sanda sun musanta cewa sun kai hari gidansa amma sun ce suna “kula da wuraren da muke ganin suna buƙatar tsaro”, inda suka ƙara da cewa suna kyautata zaton har yanzu jagoran ‘yan adawan yana gida.
“Ba mu tabbatar da cewa mun hana mutane zuwa wurinsa ba gaba ɗaya, amma ba za mu yi haƙuri da lokuta inda mutane ke amfani da gidansa don taruwa da... tada tunzura a yi tashin hankali ba,” in ji kakakin 'yansandan Kituuma Rusoke ga 'yanjarida.