| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Shugaban Uganda Museveni na kan gaba sosai a sakamakon farko na zaɓe
Museveni na fafatawa da mawakin da ya koma dan siyasa Bobi Wine mai shekaru 43, wanda shi ne ya kalubalance shi a zaben shugaban kasa na 2021.
Shugaban Uganda Museveni na kan gaba sosai a sakamakon farko na zaɓe
President Yoweri Museveni seeks to extend his 40-year rule Shugaba Yoweri Museveni na son kara wa'adin mulkinsa na shekaru 40. / AP / AP
16 Janairu 2026

Shugaban ƙasar Uganda Yoweri Museveni ne ke kan gaba a sakamakon zaɓen farko da aka sanar a ranar Jumma'a, yayin da jam'iyyar babban mai ƙalubalantarsa, Bobi Wine, ta ce shugabanta yana ƙarƙashin ɗaurin talala a gidansa.

Museni mai shekaru 81 ya mulki ƙasar Uganda tun lokacin da ya kwace mulki a shekarar 1986 kuma yana neman nasara mai muhimmanci don tabbatar da ƙarfin siyasarsa yayin da ake ta rade-radin maye gurbinsa.

Sakamakon da hukumar zaɓe ta sanar daga ƙuri'un da aka kaɗa ranar Alhamis ya nuna cewa Museveni ya samu kashi 76.25% na ƙuri'un bisa ga jimillar adadin da aka samu daga kusan rabin rumfunan zaɓe.

Wine na biye masa baya da kashi 19.85%, sauran ƙuri'un kuma sun rabu tsakanin sauran 'yan takara shida.

Museveni ya shaida wa manema labarai bayan ya kaɗa ƙuri'arsa cewa yana sa ran zai yi nasara da kashi 80% na ƙuri'un "idan babu magudi".

Zargin tafka magudi

Fitaccen mawakin nan Wine, wanda ya koma siyasa, ya yi zargin cewa an yi magudi sosai a lokacin zaben, wanda aka gudanar a karkashin katsewar intanet bayan wani gangami da rikici ya biyo bayansa.

Wine, wanda sunansa na gaskiya Robert Kyagulanyi, ya yi kira ga magoya bayansa a ranar Alhamis da su yi zanga-zanga, duk da cewa babu wata alama ta zanga-zanga zuwa yanzu.

Jam'iyyarsa ta National Unity Platform (NUP) ta rubuta a shafinta na X a daren ranar Alhamis cewa sojoji da 'yan sanda sun kewaye gidan Wine da ke babban birnin Kampala, "sun masa tsarewar talala a gida".

Kakakin 'yan sanda Kituuma Rusoke ya shaida wa Reuters cewa bai san an tsare Wine a gidan nasa ba.

Rikicin zabe

Jami’an tsaro sun tsare Wine a gidansa na tsawon kwanaki a lokacin zaben 2021 da ya wuce, inda aka ce ya samu kashi 35 na kuri’un da aka jefa.

A kalla mutum guda ne ya rasa ransa a yayin arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro, inda aka kama wasu daruruwan mutanen.. Gwamnati ta ce tana maganin duk wani mai karya doka.