Matatar mai ta Dangote ta samar da kusan kashi 20 cikin 100 na man jiragen sama da aka shigar Turai a watan Yuli, inda ta samar da fiye da tan 400,000 ga nahiyar, a cewar kamfanin Kpler da ke sa ido kan albarkatun mai a duniya.
Kazalika a watan Yuni matatar ta fitar da tan 466,000 zuwa Turai, inda Nijeriya ta zarce Amurka a matsayin babbar mai samar da man jiragen sama da ake shigarwa Turai.
Rahoton Kpler ya ce, Turai ta shigar da kimanin tan miliyan 2.06 na mai a watan Yuli, inda Dangote ke da mafi yawan kaso na man da aka shigar yankin, fiye da waɗanda suka saba kai wa wato Amurka da ƙasashen Gabas ta Tsakiya.
Alƙaluman sun nuna ƙarfin matatar na samar tare da biyan buƙatun kasuwar Turai a-kai-a-kai, yankin da ya kasance ɗaya daga cikin wuraren da aka fi buƙatar albarkatun mai a duniya.

Masu sharhi kan masana'antar man fetur sun ce matatar Dangote tana sake fasalin kasuwancin man jiragen sama a faɗin yankin Tekun Atlantika ta hanyar samar wa masu amfani da shi a Turai wata hanya ta daban ta samar da albarkatun mai.
A tsawon shekaru da dama, Turai ta dogara ne sosai kan matatun mai na Amurka da Gabas ta Tsakiya da kuma yankin Asiya.
Sai dai zaman matatar Dangote a Nijeriya da kuma gagarumin ƙarfin da take da shi na tace albarkatun mai da kuma fitar da su, ya ƙarfafa matsayinta a kasuwar man fetur ta jiragen sama a duniya.
Matatar ta ƙara yawan samarwarta
Yawan man jiragen sama da matatar ke samarwa ya kai tan 550,000 a watan Yuni, yayin da a kowace rana jigilar man ta haura zuwa ganga 660,000.
Sabon sauyin da aka samu ya zo ne a daidai lokacin da ake samun sauyi a yanayin cinikayyar makamashi a duniya, in ji Kple.
Duk da haka Turai ta ci gaba da shigar da mai mara yawa daga ƙasashen Kuwait da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Oman a watan Yuli.
Tsaikon da aka samu na katsewar wucewar albarkatun mai ta Mashigar Hormuz da kuma rashin tabbas na siyasa sun sa masu sayensa sun karkata akalarsu zuwa matatar Dangote.
Hakan ya sa matatar ta ƙarfafa rawar da take takawa a matsayin mai samar da mai a cikin babbar kasuwar, lamarin da ya ƙarfafa matsayin Nijeriya a kasuwar man ta duniya.



















