Turkiyya ta yi gargaɗi kan tsoma baki daga waje a Iran, ta buƙaci a magance rikicin a cikin gida

Kakakin Jam’iyyar AK mai mulki a Turkiyya Omer Celik ya jaddada cewa tsoma baki, musamman wanda Isra’ila take rura wutarsa, na iya jawo babban rikici da rashin zaman lafiya mai zurfi a Gabas ta Tsakiya.

By
"Ba ma bukatar ganin afkuwar duk wani irin rikici a makociyarmu Iran,” in ji Celik / AA / AA

Turkiyya ta yi gargaɗin cewa duk wani tsoma baki na ƙasashen waje a maƙwabciyarta Iran zai ta'azzara rikice-rikice a ƙasashen biyu da kuma yankin Gabas Ta Tsakiya baki ɗaya, tana mai jaddada cewa ya kamata a warware matsalolin cikin gida na Iran ta hanyar tattaunawa da kuma yanayin zamantakewa na ƙasar.

Mataimakin Shugaban Jam'iyyar AK kuma Kakakin Jam'iyyar Omer Celik ya bayyana a ranar Litinin cewa Ankara ba ta son ganin rikici a Iran, duk da cewa ta amince cewa akwai matsaloli a cikin al'ummar Iran da ma a cibiyoyin gwamnati.

"Ba ma son wani rikici ya ɓarke ​​a maƙwabciyarmu Iran," Celik ya faɗa a wani taron manema labarai a hedkwatar jam'iyyar da ke Ankara bayan taron da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jagoranta.

Ya ce, kamar yadda shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya faɗa, ya kamata a warware matsalolin Iran ta hanyar yanayin cikin gida na al'ummar Iran da kuma aniyar ƙasa ta ƙasar.

Ƙaruwar rikici

"Shiga tsakani na ƙasashen waje zai haifar da mummunan sakamako," in ji Celik, yana mai ƙarawa da cewa musamman tsoma bakin da Isra'ila ke azalzalowa zai iya haifar da manyan rikice-rikice da rashin kwanciyar hankali a yankin.

Da yake jaddada cewa ya kamata a magance matsalar ta hanyar tattaunawa, sulhu da kuma ƙara tuntubar juna, Celik ya ce kalaman da jami'an Isra'ila suka yi kwanan nan game da Iran na iya haifar da rura wutar rikicin yankin.

"Wannan bakar hanyar za ta haifar da tashin hankali a duk faɗin yankin kuma dole ne a yi watsi da ita gaba ɗaya," in ji shi.

A halin yanzu Iran na fuskantar zanga-zanga mafi girma tun 2022, yayin da shugaban Amurka Donald Trump ya ce Washington za ta iya shiga tsakani idan aka yi amfani da ƙarfi a kan masu zanga-zanga, wanda hakan ke ƙara nuna damuwa game da tabarbarewar rikicin.