| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Amurka da Isra'ila sun kai sababbin hare-hare a Iran
Isra'ila ta ayyana dokar ta-ɓaci a faɗin ƙasar bayan ta kai hari Iran a yayin da ake tsaka da tattaunawa da Amurka.
Amurka da Isra'ila sun kai sababbin hare-hare a Iran
Hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniyar Tehran, babban birnin Iran ranar Asabar, 28 ga Fabrairun 2026. / AP
17 awanni baya

Ministan Tsaron Isra'ila Israel Katz ranar Asabar ya ce ƙasarsa da haɗin gwiwar Amurka sun kai "hare-haren kandagarki" a Iran, saboda abin da ya kira barazanar da take yi ga tsaron ƙasarsu.

Kazalika Katz ya ayyana dokar ta-ɓaci ta ƙasa baki ɗaya, sannan ya yi kira ga 'yan ƙasar su bi umarnin rundunar soji ta Home Front Command wadda ke da alhakin kare fararen-hula.

"Ƙasar Isra’ila ta kai harin kandagarki a Iran. Ministan Tsaro Israel Katz ya ayyana dokar ta-baci ta musamman a duka ƙasar," a cewar wata sanarwa daga ma’aikatar tsaron ƙasar.

Masu AlakaTRT Afrika - Jirgin ruwa mafi girma a duniya mai ɗauke da filin jirgin sama na Amurka ya isa gaɓar tekun Isra'ila

Ganau sun ce sun ji manyan ƙararraki na fashewar abubuwa a Tehran, inda hayaƙi ya mamaye sararin samaniya, ko da yake kawo yanzu Iran ba ta yi martani ba.

An ji ƙarar fashe-fashe a Isfahan, Qom, Karaj da Kermanshah, a cewar kamfanin dillanacin labarai na Fars News Agency.

Hare-haren na zuwa ne a yayin da ake tattaunawa tsakanin Amurka da Iran sakamakon zaman ɗarɗar kan shirin Iran na mallakar makaman nukiliya.

Rundunar sojin Isra’ila ta fitar da sanarwa inda ta yi kira ga ‘yan ƙasar su yi kaffa-kaffa, tana mai gargaɗi game da yiwuwar hare-hare na makamai masu linzami.

Ta sanar da rufe "dukkan makarantu da hana tarukan jama’a da zuwa wurin aiki."

Shirin kawar da ɗaukacin shugabannin Iran

Amurka tana da hannu a hare-haren da Isra’ila ta kai wa Iran, a cewar shugaban Amurka Donald Trump a jawabin da ya yi bayan kai harin.

Ya ce babban burinsu shi ne kawar da ɗaukacin shugabannin Iran tare da bai wa ‘yan ƙasar damar kafa sabuwar ƙasa.

Harin farko ya faɗa kusa da ofishin Shugaban Addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Babu cikakken bayani a kan ko Khamenei, mai shekara 86, yana ofis a lokacin. Wani jami’in gwamnati ya shaida wa Reuters an fitar da shi zuwa wani wuri mai aminci da ke wajen Tehran.

Wani jami’in Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters an kai hare-haren ne ta sama da ta ruwa.

Iran da Isra’ila sun sanar da rufe sararin samaniyarsu.