Gwamnatin Tarayya Nijeriya ta yi ƙarin haske kan ce-ce-ku-cen da ake yi a ƙasar game da rashin halartar Shugaba Bola Tinubu babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na 81 a birnin New York.
Shugaba Tinubu ya bai wa Mataimakinsa Kashim Shettima umarnin wakiltarsa da kuma jagorantar tawagar Nijeriya zuwa babban taron zauren MDD.
Ana sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasar zai gabatar da jawabin Nijeriya tare da halartar tarurruka masu muhimmanci da tattaunawa kai-tsaye da shugabannin ƙasashen duniya da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da kuma abokan hulɗa wajen ci-gaba.
Wannan shi ne karo na uku a jere da Tinubu ya tura mataimakinsa don ya wakilce shi a babban taron; matakin da ya haifar da martani daga manyan shugabannin 'yan’adawa, musamman tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, wanda ya buƙaci Shugaban Kasar ya yi wa 'yan Nijeriya bayani kan dalilin rashin halartarsa.
Sai dai, a cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama'a na Nijeriya, Mohammed Idris, ya sanya wa hannu a ranar Litinin, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Nijeriya za ta samu wakilci yadda ya kamata a tsawon lokacin taron mai muhimmanci.
Sanarwar ta jaddada cewa Shettima na da cikakken ikon wakiltar Shugaban Ƙasa da kuma Tarayyar Nijeriya baki ɗaya.
"Ayyukansa a New York za su inganta manufofin Nijeriya kan batutuwan zaman lafiya da tsaro, da ci-gaban tattalin arziki, da matakan magance sauyin yanayi, da sake fasalin tsarin hada-hadar kuɗi na duniya, da ci-gaba mai dorewa, da kuma haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa," in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa ‘‘a halin yanzu Tinubu yana hutun shekara,’’ inda ta jaddada cewa matakin da ya ɗauka na bai wa Mataimakin Shugaban Ƙasa jagorancin tawagar Nijeriya ba sabon abu ba ne, kuma ba ya rage darajar diflomasiyyar ƙasar.
"Gwamnatin Tarayya ta lura da kalaman siyasa na baya-bayan nan daga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da kuma wata ƙungiyar fafutuka ta Amurka da ya ɗauka aiki, waɗanda ke tambaya kan rashin halartar Shugaba Tinubu tare da ƙoƙarin danganta hakan da dalilai na karya mara sa tushe.
"Nijeriya na daraja daɗen dangantakarta da Amurka, wadda ta ƙunshi cinikayya da zuba hannayen-jari da haɗin gwiwa a fannin tsaro da makamashi da cibiyoyin dimokuraɗiyya da kwanciyar hankali a yanki da kuma alaƙar da ke tsakanin mutane da mutane.
"Wannan dangantaka ana gudanar da ita ne ta hanyoyin diflomasiyya da na gwamnati kuma bai kamata a rikita ta da sharhin jam'iyya ko ayyukan ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a madadin abokan hulɗar siyasa ba."
A ƙarshe sanarwar ta Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi kira ga 'yan ƙasar da kafafen watsa labarai da su yi ƙokari wajen iya tantance bayanai da aka tabbatar, da ra'ayin siyasa na gaskiya da kuma hasashe mara tushe.





















