An kashe ’yanbindiga 20 a harin da aka kai sansanin sojojin sama a Nijar: Ma’aikatar Tsaro
Jami’an tsaron filin jirgin saman da taimakon dakarun da ke tsaron birnin Yamai sun mayar wa ’yanbindiga martani cikin “hanzari da ƙwarewa”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
An kashe ’yanbindiga aƙalla 20 wasu kuma 11 suka jikkata bayan wani hari da aka kai sansanin sojin sama na Air Base 101 a Babban Birnin Jamhuriyar Nijar, Yamai da sanyin safiyar ranar Alhamis, in ji sanarwar da Ma’aikatar Tsaro ta Ƙasar ta fitar.
Sanarwar ta ce da misalin karfe 12:20 na dare a ranar Alhamis wasu ’yanbindiga a kan babura sun kai hari sansanin sojojin wanda yake kusa da filin jirgin saman Diori Hamani.
Jami’an tsaron filin jirgin saman da taimakon dakarun da ke tsaron birnin Yamai sun mayar wa ’yanbindiga martani cikin “hanzari da ƙwarewa”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
’Yanbindigar sun lalata wani wajen ajiye makamai da ke sansanin bayan da gobara ta tashi a wajen. Kazalika sun lalata wasu jiragen sama waɗanda ba na soji ba da ke ajiye filin jirgin saman birnin.
Sannan sanarwar ta ce babu wanda ya rasa ransa daga ɓangaren dakarun ƙasar, ko da yake ta ce akwai mutum da suka jikkata kuma an garzaya da su asibiti nan-take.
Ma’aikatar Tsaron Ƙasar ta buƙaci al’umma su riƙa sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a kusa da su, kuma su sanar da jami’an tsaro wani ko wasu da ba su yarda da take-takensu ba.