An ji ƙarar harbe-harbe da fashewar wasu abubuwa a cikin daren Alhamis kusa da Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, lamarin da ya ɗaga hankulan mazauna birnin.
Wasu bidiyo da aka wasu mazauna birnin suka ɗauka ya nuna yadda sararin saman birnin ya yi haske yayin da fashewar wasu abubuwa ta rika biyo baya.
Sannan akwai wasu hotuna da suka nuna wuta na ci da kuma yadda wasu mototoci suka ƙone ƙurmus.
Mazauna birnin waɗanda suke maƙwabtaka da Filin Jirgin Saman Diori Hamani sun ce an kwashe tsawon sa’o’i biyu ana jin ƙarar harbe-harben kafin daga bisani su lafa. Zuwa misalin karfe biyu na dare ne abin ya lafa.
Filin jirgin saman yana da nisan kilomita 10 daga fadar shugaban kasa kuma kusa da fadar akwai sansanin sojin soji da wasu manyan cibiyoyin soji.
Kuma a nan ne hedkwatar rundunar haɗin gwiwa ta tsaro mai dakaru daga ƙasashen Nijar da Burkina Faso da Mali don yaƙi damasu ikirarin jahadi a yankin Sahel.
Har zuwa safiyar ranar Alhamis mahukunta a ƙasar ba su bayyana dalilin da ya jawo harbe-harben ba ko kuma adadin mutanen da suka jikkata ba. Mazauna birnin da dama sun ce sun ji ƙarar jiniya yayin da motocin ’yan kwana-kwana suke zuwa filin jirgin saman da sanyin safiya.
Nijar tana ƙarƙashin mulkin soji tun shekarar 2023 karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tiani, bayan ya hamɓarar da gwamnatin farar-hula ta Mohamed Bazoum. Tuni gwamnatin sojin ƙasar ta raba gari da Faransa da Amurka waɗanda suke taimaka wa ƙasar wajen yaƙi da ’yan ta’adda.













