An gano aƙalla gawarwakin mutane 61 ciki har da na jami’an tsaro da na farar-hula da aka kashe a wani harin ‘yan fashin daji da ya faru ranar Talata a garin Bagna da Erena a ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja a Nijeriya.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa mazauna yankin ne suka kwaso gawarwakin daga dazukan da ke zagaye da su, kwanaki bayan afkuwar mummunan lamarin da ya haɗa da satar mutane.
Sai dai zuwa yanzu gawarwakin farar-hula kawai aka binne a Erena, yayin da aka ajiye na jami’an tsaro a mutuwaren Babban Asibin Gwamnati da ke Minna.

A cewar jaridar, wani mazaunin yankin na Erena ya shaida cewa waɗanda abin ya rutsa da su sun haɗa da ‘yan bijilante, da jami’an tsaro na ƙasa, da kuma farar-hula.
Sai dai hukumomin ‘yansanda sun tabbatar da kisan ‘yansintiri guda uku ne kacal, kamar yadda jaridar ta ambato.
Duk da cewa mazauna garin sun yaba wa yunƙurin jami’an tsaro da suka kawo ɗauki bayan zuwan maharan har suka kore su, sun kuma soki gwamnati kan gaza ɗaukar mataki bayan samun bayanan sirri da zai iya hana faruwar harin.
Harin dai ya janyo rasa matsuguni inda ɗaruruwan mazauna yankin suka nemi mafaka a makarantar Zumba Central Primary School da wasu wurare a Shiroro LGA.















