Rundunar ‘yansandan Jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya ta ce ta gano wani bam da bai fashe ba a ƙauyen Zugurma na ƙaramar hukumar Mashegu.
Jami'in Hulɗa da Jama'a na rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a Minna ranar Talata.
Ya ce an gano nakiyar ce bayan wani rahoto da aka samu a ranar Litinin daga Jami'in 'yansanda na Yankin Ibbi da ke Mashegu.
Ya ƙara da cewa wasu mazauna yankin sun ga wani abu da ake zargin bam ne a cikin wani daji da ke yankin.
Abiodun ya ce jami'an 'yansanda na yankin sun yi gaggawar zuwa wurin da lamarin ya faru inda suka killace yankin don tabbatar da tsaron mutane.

Ya ce Kwamishinan 'Yansandan jihar, Adamu Elleman, ya ba da umarnin tura jami'ai zuwa wajen.
Kakakin 'yansandan ya ce sashen kwance bamabamai na rundunar, wanda CSP Mohammed Mamun ke jagoranta, ya ziyarci wajen a ranar Talata.
Abiodun ya ƙara da cewa jami'an rundunar, tare da al'ummar yankin sun jagoranci tawagar zuwa daidai wurin da aka gano abin.
"Tawagar ta kwance bam ɗin sannan ta miƙa shi ga hedikwatar 'yansandan jihar da ke Minna," in ji shi.
Abiodun ya bayyana cewa an soma gudanar da bincike domin gano inda bam ɗin ya samo asali, yana mai tabbatar da cewa za a fitar da ƙarin sabbin bayanai a kan lamarin nan ba da jimawa ba.
Ya ƙara da cewa Kwamishinan 'yansanda Jihar Neja ya yi kira ga jama'ar yankin su kwantar da hankalinsu, yana mai jaddada cewa dukkan hukumomin tsaro suna nan don tabbatar da tsaro da dawo da zaman lafiya a yankin da kewayensa.





















