Amurka za ta tura dakaru 200 Nijeriya domin horas da dakarun sojin ƙasar a yaƙinsu da ƙungiyoyin ‘yanta’adda, kamar yadda jami’an Nijeriya da na Amurka suka bayyana ranar Talata.
Hakan na faruwa ne yayin da Amurka ke ƙara ƙulla alaƙa ta soji da ƙasar da ke Yammacin Afirka.
"Za mu tura dakarun Amurka su taimaka wajen horaswa da taimako na fasaha," kamar yadda Manjo Janar Samaila Uba, magana da yawun rundunar tsaron Nijeriya ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.
Jaridar Wall Street Journal ta ba da rahoto kan shirin tura sojojin, wanda zai yi aiki tare da wata ƙaramar tawagar sojojin Amurka da ke ƙasar don taimaka wa Nijeriya waje kai hare-hare ta sama kan ‘yanta’adda.

Sojojin, waɗanda ake sa rai za su isa ƙasar cikin makonni kaɗan masu zuwa, za su ba da “horo da kuma shawara ta fasaha," ciki har da taimaka wa takwarorinsu na Nijeriya wajen jagorantar ayyuka da suka haɗa da hare-hare ta sama da ƙasa a lokaci ɗaya , in ji jaridar.
Mai magana da yawun sashen rundunar Afirka ta sojin Amurka ya tabbatar da bayanan cikin rahoton ga kamfanin dillancin labaran AFP.
Nijeriya tana fama da shan matsin lamba ta diflomasiyya daga Amurka game da rashin tsaro a ƙasar, wanda Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a matsayin "zalunci" da "kisan kiyashi " kan Kiristoci.
Duk da cewa akwai lokutan da ake kai hari kan Kiristoci kaɗai, amma bayanai sun nuna cewa an fi kashe Musulmai, inda babban mai bai wa Trump shawara game da harkokin Larabawa da Afirka Massad Boulos yake cewa a shekarar da ta gabata Boko Haram da Daesh "sun kashe Musulmai fiye da Kiristoci."
Abuja ta yi watsi da zarge-zarge yi wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya.











