| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Amurka ta kai hare-hare a Tsibirin Qeshm na Iran: Rahoto
Jami’an Amurka sun bayyana hare-haren a matsayin matakan kariya, inda suka ce an kai su ne domin hana Iran samun damar kai hari kan jiragen kasuwanci da ke bi ta Mashigar ruwan Hormuz.
Amurka ta kai hare-hare a Tsibirin Qeshm na Iran: Rahoto
Amurka ta kai hari kan tsibirin Qeshm na Iran a daidai lokacin da ake ƙoƙarin farfaɗo da tattaunawar diflomasiyya — Reuters

Amurka ta kai hare-hare kan Tsibirin Qeshm na Iran, kamar yadda jaridar The Wall Street Journal ta ruwaito, tana mai ambato wasu jami’an gwamnatin Amurka.

Rahotannin sun ce an kai hare-haren ne a ranar Litinin, a daidai lokacin da Shugaba Donald Trump ke ƙoƙarin rage fargabar yiwuwar sake ɓarkewar babban rikicin soji tsakanin Amurka da Iran a yayin da ake shirin gudanar da zaɓen tsakiyar wa’adin majalisar dokokin Amurka a ranar Talata.

“Wannan matakin kariya ne da aka ɗauka a kan Iran wadda ta yi amfani da makamai masu linzami masu yawa wajen kai hare-haren sama kan kadarorin Amurka,” kamar yadda wani jami’in Amurka ya bayyana.

“Mun yi yaƙi da Iran. Mun yi nasara,” kamar yadda Trump ya shaida wa manema labarai da safiyar ranar, yana mai ƙari da cewa, “Ban ma san ko za a iya kiran abin da ya faru da yaƙi ba, domin ba mu fafata ba tsawon watanni.”

Sai dai wasu jami’an Amurka sun shaida wa jaridar The Wall Street Journal cewa sojojin Amurka sun ci gaba da kai ƙananan hare-hare kan wasu wurare a Iran tsawon makonni.

A cewar rahoton, wasu jami’an Amurka sun bayyana hare-haren a matsayin matakan kariya da aka ɗauka domin hana Iran samun ƙarfin da zai ba ta damar yin barazana ko kai hari kan jiragen kasuwanci da ke wucewa ta Mashigar ruwan Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci ga harkokin sufuri da cinikayyar duniya.

Masu AlakaTRT Afrika - Trump na so a kawo ƙarshen yaƙin Iran ta diflomasiyya, Netanyahu ya ce a kai ƙarin hare-hare: rahoto

An ji a ƙarar fashe-fashe da sanyin safiyar ranar Talata a kudancin ƙasar, ciki har da Tsibirin Qeshm da birnin Bandar Lengeh da ke gaɓar teku, a cewar rahotannin da kamfanonin dillancin labaran Iran suka ruwaito.

Trump ya rage fargabar sake ɓarkewar yaƙi

A ranar Litinin, Trump ya yi watsi da yiwuwar sake kai hare-haren soja kan Iran bayan zaɓen tsakiyar wa’adin majalisar dokoki ta Amurka, yana mai cewa ƙoƙarin diflomasiyya na samun ci gaba.

A yayin tambayar da wani ɗanjarida ya yi wa shugaban na Amurka kan ko yana shirin kai ƙarin hare-hare kan Iran bayan zaɓen, Trump ya amsa da cewa, “A’a.”

Trump ya jaddada ewa Iran ba za ta taɓa mallakar makaman nukiliya ba, yana mai cewa jami’an Iran sun riga sun fahimci matsayar Amurka kan wannan batu.

Ya ce, hana Tehran mallakar ƙarfin nukiliya na da muhimmanci matuƙa, yana mai gargaɗin cewa ƙasar ba za ta iya ci gaba da tafiyar da al’amuranta kamar yadda take yi a yanzu ba idan ta samu irin wannan ƙarfin.

“Mun dakatar da hakan a shekarar da ta wuce ta hanyar amfani da manyan jiragen yaƙinmu samfurin B-2, waɗanda suka kai hari kan dukkan wuraren kuma suka binne komai a ƙarƙashin ɗaruruwan tan na duwatsu,” in ji Trump.

Shugaban Amurkan ya kuma nuna cewa tattaunawar diflomasiyya na tafiya yadda ya kamata, yana mai danganta yiwuwar cim ma yarjejeniya da raguwar farashin makamashi.

“Wataƙila hakan ne ya sa farashin mai ya faɗi sosai” in ji shi.

Rumbun Labarai
Pentagon ta ce yaƙin Iran ya laƙume dala biliyan 47
Jagoran adawa a Isra’ila ya nemi haɗin gwiwar jam’iyyun Larabawa domin kawar da Netanyahu daga mulki
Abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da zaben Isra’ila da me yake nufi ga Falasdinawa
Iran ta zargi Amurka da rashin gaskiya a tattaunawa, tana mai cewa tana ƙoƙarin tilasta mata buƙatu
Manyan jami’an Turkiyya, Saudiyya da Pakistan za su ziyarci Iran don tattauna batutuwan tsaro
Mayaƙan Houthi sun kai hari filin jiragen Riyadh, ƙawancen Saudiyya ta kai hari kan rokokin Sanaa
Netanyahu ya bayar da umarnin kulle yankin Yammacin Kogin Jordan da kuma rufe Hebron gaba ɗaya
Trump ya ce Amurka za ta iya kai wa Iran sabbin hare-hare
Turkiyya ta kawar da yunkurin jan kasar cikin yake-yaken yankin: Erdogan
WFP ta rage yawan tallafi a Gaza ga mutane 500,000 sakamakon mamayar Isra’ila a yankin
Iran ta ce Netanyahu na ingiza Amurka ga wani yaƙi don kauce wa zaman kurkuku
Tankar mai dauke da ganga fiye da miliyan biyu ta kama da wuta a Mashigar Hormuz
Sojojin Yemen sun kama tawagar masu sarrafa jiragen yaƙi marasa matuƙa na Houthi a Taiz
Mutum 5 sun mutu a hare-haren makamai masu linzami na Houthi a fadar shugaban ƙasar Yemen
An harbo makami mai linzami a sararin samaniyar yankin Madina: Sojojin Ƙawance na Saudiyya
Tarkacen makamai masu linzami na ‘yan Houthi sun jikkata mutum 4, sun lalata gidaje 15 a Saudiyya
Nijeriya ta yi Allah wadai da harin Houthi kan filin jiragen sama na Riyadh a Saudiyya
'Yan Houthi sun kai ƙarin hare-hare a filin jirgin saman Sarki Khalid da ke Riyadh
Mutum 12 sun rasu, 309 sun jikkata bayan harin mayakan Houthi a filin jirgin Riyadh na Saudiyya
Iran na nazarin martanin Amurka kan shirin kwanaki bakwai na sake buɗe Mashigar Hormuz