MDD ta ayyana cinikin bayi a Afirka a matsayin ‘laifi mafi muni ga ɗan'adam'
Ƙudurin ya yi kira ga ƙasashen da suke da hannu a harkar cinikin bayin da su yi adalci ta fuskar gyara kuskuren, wanda ya haɗa da neman afuwa a hukumance, biyan diyya, da kuma ɗaukar matakan yaƙi da nuna bambancin jinsi.
Babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya ayyana cinikin bayin Afirka ta tekun Atalantik a matsayin “babban laifi mafi muni da aka yi wa ɗan’adam,” wani abu da masu fafutuka suka yaba da shi a matsayin matakin farko na gyara raunuka da kuma yiwuwar biyan diyya.
An amince da ƙudurin ne a ranar Laraba cikin tafi, inda ƙasashe 123 suka kaɗa ƙuri’ar amincewa; ƙasashe uku suka ƙi amincewa (Amurka, Isra’ila, da Argentina); yayin da ƙasashe 52 suka ƙi kaɗa ƙuri’a, ciki har da Burtaniya da ƙasashen Tarayyar Turai.
“Cinikin bayin Atalantik wani laifi ne ga bil’adama wanda ya taɓa mutuncin ɗan’adam, ya wargaza iyalai, sannan ya lalata al’ummomi,” in ji Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres.
“Domin halatta abin da ba za a taɓa iya halastawa ba, masu goyon bayan bautar da waɗanda suka ci gajiyar abin sun karkata akalar nuna wariyar launin fata zuwa wani nau’in ilimin kimiyyar ƙarya.”
Ƙudurin ya wuce gaban batun amincewa da laifin, domin ya buƙaci ƙasashen da suke da hannu a cinikin bayin da su yi adalci ta fuskar gyara kuskure, gami da ba da haƙuri a hukumance, biyan diyya, da ɗaukar matakan shawo kan nuna bambancin launin fata da ya daɗe yana faruwa.
Haka kuma, ƙudurin ya yi kira da a “gaggauta mayar da kayayyakin tarihi” ba tare da wata tangarɗa ba, kamar ayyukan fasaha, gumaka da wasu takardu muhimmai zuwa ƙasashensu na asali.
John Dramani Mahama, shugaban ƙasar Ghana kuma babban mai fafutukar neman a biya diyyar, ya yi jawabi a gaban zauren majalisar kafin kaɗa ƙuri’ar, inda ya bayyana ƙudurin a matsayin wani mataki na warkar da raɗaɗin baya.
“A yau, mun taru ne cikin haɗin kai don tabbatar da gaskiya da kuma neman hanyar waraka da adalci da gyara,” in ji shi, tare da ƙara da cewa hakan zai zama “kandagarki ga mantuwa.”
Rubutun ƙudurin ya yi Allah wadai da “safara da bautar da ’yan Afirka a matsayin kadarori,” sannan ya nuna irin illolin da bautar ta bari har yau, waɗanda suka hada da nuna wariyar launin fata da kuma tsarin da ya kira mulkin mallaka na zamani.
Ana ƙarfafa gwiwar ƙasashen da su gudanar da tattaunawa kan batun adalci da biyan diyya, sannan su goyi bayan shirye-shiryen ilimantarwa game da tarihin cinikin bayin na Atalantik.
Ƙudurin ya kuma bukaci haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyoyin yanki kamar Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU), Ƙungiyar Ƙasashen Caribbean (CARICOM), da Ƙungiyar Ƙasashen Amurka (OAS) domin ciyar da ƙoƙarin gyara kuskuren gaba.