| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Iran ta tabbatar da kisan Ali Khamenei da iyalansa
Tehran ta sha alwashin yin ramuwar gayya kan kisan da aka yi wa jagoran addinin ƙasar Iran, sannan ta sanar da yin makokin kwana 40.
Iran ta tabbatar da kisan Ali Khamenei da iyalansa
Tehran ta sha alwashin yin ramuwar gayya kan kisan da aka yi wa jagoran addinin ƙasar, sannan ta sanar da yin makokin kwana 40. / TRT Balkan

Kafar watsa labaran gwamnatin Iran ta ce an kashe Jagoran Addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei a harin da Isra'ila da Amurka suka kai, lamarin da ya sanya kiraye-kiraye ga rundunar juyin-juya-hali ta Revolutionary Guards domin ta ɗauki matakin ramuwar gayya.

Gidan talbijin na ƙasar Iran ranar Lahadi ya sanar da makokin kwana 40 tare da bayar da hutun kwana bakwai bayan kisan shugaban addinin ƙasar mai shekara 86, wanda ke kan mulki tun shekarar 1989.

Kafofin watsa labaran Iran sun ruwaito cewa an kashe ‘yar Ayatollah Ali Khamenei da jikarsa da kuma surukinsa a harin.

Masu AlakaTRT Afrika - Iran ta musanta iƙirarin Amurka da Isra'ila na kashe Jagoran Addini Ali Khamenei

"Shahadar da shugaban addini ya yi ba za ta sa a manta da tafarkinsa da jagorancinsa ba, hasali ma, za a tabbatar da su ne bisa ƙarfin gwiwa da jajircewa," a cewar mai gabatar da labarai a gidan talbijin na gwamnatin Iran.

Rundunar juyin-juya-hali ta Revolutionary Guards ta sha alwashin yin ramuwar gayya kan “wadanda suka kashe” Khamenei.

"Rayuwar gayya da ƙasar Iran za ta yi zai kasance mai tsanani kuma cike da karsashi, sannan waɗanda suka kashe Shugaban Al’umma ba za su ci bulus ba," in ji wata sanarwa da Rundunar juyin-juya-hali ta fitar.

An kashe jagoran addinin Iran lokacin da yake taro da na hannun damansa

Harin da Isra’ila da Amurka suka kai Iran ranar Asabar ya zo ne a lokacin da Khamenei yake gudanar da taro da manyan masu ba shi shawara, a cewar wsu majiyoyi na gwamnatin Amurka.

Isra’ila ta yi iƙirarin cewa an kashe Khamenei ne tare da manyan na hannun damansa da suka haɗa da Ali Shamkhani, tsohon sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa, da Mohammad Pakpour, kwamandan
Rundunar juyin-juya-hali ta Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC).

Rumbun Labarai
Iran da Oman sun amince kan hanyar gudanar da Mashigar Hormuz, in ji Tehran
Ministocin ƙasashen Larabawa da na Musulmai sun haɗu a Jordan don ɗaukar matsaya kan Gabashin Ƙudus
Yaƙin Iran na neman karar da makamai masu linzami na Amurka: rahoto
'Yansandan Dubai sun rufe shafukan sada zumunta 103 na bogi a ƙoƙarinsu na yaƙi da zamba
Trump ya buƙaci Iran ta ƙulla yarjejeniya da Amurka ko ta miƙa wuya
Shin za a amince cewa Netanyahu zai girmama yarjejeniyar janyewar Isra’ila baki daya daga Gaza?
Trump ya ce Amurka da Iran za su soma sabuwar tattaunawa a ranar Litinin
Pentagon ba ta da ƙarfin sojin ruwa na kare Isra'ila: Janar ɗin sojin Amurka
Saudiyya ta kammala shirye-shiryen kafa Ƙawancen Tsaron Teku tare da goyon bayan ƙasashe 14
Trump ya ce kwamitin sulhu na Gaza ya yarda Hamas ta ajiye makamai da janyewar Isra'ila daga yankin
Iran ta yi ikirarin lalata jiragen yaƙin F-35 na Amurka a Jordan
Amurka ta kai wa Iran sabbin hare-hare, in ji CENTCOM
Isra'ila ta kashe dala miliyan 46.5 wajen ƙoƙarin sa AI ya yaɗa ra'ayoyinta kan yaƙin Gaza
Amurka da Saudiyya sun kai hari kan ƙungiyar da ke goyon bayan Iran a Iraki
Iran ta ce babu kyakkyawan yanayin da ya dace ta tattauna da Amurka duk da suna musayar saƙonni
Trump ya dakatar da kai wa Iran hari saboda karancin makaman tsaron samaniya — rahoto
An kai wa ma'aikatan jiragen ruwan India hari kusa da mashigar Hormuz
Iran ta yi watsi da tayin tsagaita wuta da Amurka ta yi mata - rahoto
Houthi ta gargaɗi kamfanonin jigilar kaya su guji amfani da tashoshin jiragen ruwa na Saudiyya
IRGC ta Iran ta yi ikirarin kai hari kan jiragen saman Amurka a Jordan