‘Yanta’adda masu alaƙa da al Qaeda da Daesh suna ƙara kai hare-hare cikin sauri a kan iyakokin Nijar da Benin da Nijeriya, lamarin da ke ta’azzara yanayin tsaron ƙasashen, in ji wata ƙungiya mai sa ido kan rikice-rikice.
Hare-hare masu alaƙa da ƙungiyoyin ‘yanta’dda a yankin kan iyakokin ƙasashen uku sun ƙaru da kashi 90 cikin 100 tsakanin shekarar 2024 da shekarar 2025 yayin da mace-mace suka ruɓanyawa inda fiye da mutum 1,000 suka mutu yayin da ƙungiyoyin suka zafafa kai hare-hare, in ji wani rahoton ƙungiyar ACLED mai sa ido kan rikicie-rikice da aka wallafa ranar Alhamis.
Sakamakon binciken ya nuna yadda ƙungiyoyin ‘yanta’adda ke bazuwa a Yammacin Afirka, inda gwamnatoci da kuma sojojin ƙetare suka shafe fiye da shekaru goma suna ƙoƙarin daƙile yaɗuwarsu.
Rahoton ya ce mayaƙa da ke da alaƙa da al Qaeda da Daesh sun ƙarfafa zamansu a ƙananan hukumomin Alibori da Borgou na Jamhuriyar Benin da lardin Dosso na Nijar da kuma jihohin Kebbi da Neja da Kwara na Nijeriya.
Aika-aikarsu a halin yanzu na " ci gaba da yaɗuwa da ƙara haɗari da kuma ƙarin barazana ga fararen-hula," in ji rahoton.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewa sojojin Nijeriya da gwamnatocin Jamhuriyar Nijar da Benin ba su mayar da martani ga buƙatar yin tsokaci kan binciken ba.
‘Yan bindiga suka faɗaɗa a arewa maso yammacin Nijeriya
Nijeriya ta shafe fiye da shekaru 15 tana yaƙar ‘yanta’adda - yawancinsu ‘yan Boko Haram da ISWAP a arewa maso gabashin ƙasar. Amma al Qaeda‑ da ƙungiyoyi masu alaƙa da IS suna ƙara aika-aika a arewa maso yammacin Nijeriya, inda dazuka masu yawa da kuma kasancewar madafun iko masu rauni suka samar musu wani yanayi na ɓunƙasa.
Yammacin Afirka ya kasance wani wuri da wasu ɓangarorin masu iƙirarin jihadi suke inda da yawa daga cikinsu suke aika-aika a ƙarƙashin ƙungiyar Jama'at Nusrat al‑Islam wal‑Muslimin (JNIM) mai alaƙa da al Qaeda da kuma ƙungiyar IS a Sahel (ISSP) mai alaƙa da IS.
Faɗaɗa aika-aikarsu ya janyo rashin ɗorewar harkokin siyasa a faɗin yankin.
Sojoji sun ƙwace mulki a ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar tun shekarar 2020, inda suka kafa hujja da gazawar gwamnatocin da aka zaɓa wajen daƙile tashin hankali.
Sojojin da suka kitsa juyin mulkin da ya yi rashin nasara a Benin cikin watan Disamba su ma sun kafa hujja ne da rashin tsaro.
Amurka ta ƙaddamar da hare-haren sama a arewa maso yammacin Nijeriya a watan Disamba kuma ta fara tura sojoji domin horas da dakarun Nijeriya da ke yaƙar ‘yanbindiga.
Matakan haɗin gwiwa sun yi rauni a ‘yan shekarun baya bayan nan yayin da Nijar da Burkina Faso da Mali suka janye daga ƙungiyoyin yankin, lamarin da ke zagon ƙasa ga ayyukan tsaro na haɗin gwiwa.
ACLED ta ce ƙungiyoyin ‘yanta’adda sun matsa ƙaimi wajen fitar da bayanai game da aika-aikarsu a yankin na kan iyakokin ƙasashen uku, wani lamari da zai iya nuna gasa tsakanin ɓangarori masu hamayyar. Irin wannan "rige-rigen," kamar yadda rahoton ya bayyana , zai iya sa lamarin ya daɗa ƙamari.














