| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Kotun Sudan ta yanke wa shugaban RSF Hemedti hukuncin kisa kan kashe tsohon gwamnan Darfur ta Yamma
Kotun da ke yaƙi da ayyukan ta'addanci ta yanke wa shugabannin RSF hukuncin laifukan yaƙi da cin zarafin bil'adama da kisan ƙare-dangi da kuma kisan gillar da aka yi wa tsohon gwamnan Darfur ta Yamma Khamis Abdallah Abakar a shekarar 2023.
Kotun Sudan ta yanke wa shugaban RSF Hemedti hukuncin kisa kan kashe tsohon gwamnan Darfur ta Yamma
Kotun Sudan ta yanke wa Mohamed Dagalo, shugaban rundunar RSF, hukuncin kisa a bayan idonsa a ranar 12 ga Yuli, 2026.

Wata Kotun yaƙi da ta'addanci a Sudan ta yanke wa shugaban rundunar dakarun sa-kai ta RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, hukuncin kisa a bayan idonsa kan kashe tsohon gwamnan Darfur ta Yamma Khamis Abdallah Abakar.

Kazalika kotun a Port Sudan ta yanke wa mataimakin shugaban RSF, Abdel Rahim Hamdan Dagalo, ɗan’uwan ​​Hemedti, da wasu mutane 14 hukuncin kisa a bayan idanunsu.

Hukuncin ya zama irinsa na farko da wata kotu ta yanke wa shugaban RSF tun lokacin da rikici da ya ɓarke tsakanin sojojin Sudan da rundunar RSF a watan Afrilun 2023.

Kotun ta yanke wa waɗanda ake tuhuma hukuncin kisa kan zarge-zargen da suka haɗa da aikata laifukan yaƙi da cin zarafin bil'adama da kisan ƙare-dangi da kuma laifukan da suka shafi hakkin mutane da kadarorinsu.

Haka kuma, ta yanke wa Hemedti hukuncin kisa kan shiryawa da kuma aiwatar da laifuka yayin da shi kuma mataimakinsa aka yanke masa hukuncin kisa bisa haɗa kai wajen aikata mummunar aika-aika.

Munanan ayyukan ta'addanci

Daga cikin waɗanda ake tuhuma akwai Algoney Hamdan Daglo Musa, wanda aka fi sani da Al-Qoni, shi ma ɗan’uwa ne na ​​Hemedti; da Abdel Rahman Juma, kwamandan RSF a jihar Darfur ta Yamma da kuma shugaban ƙabila Al-Tijani Al-Tahir Karshoum.

An kashe Abakar ne a ranar 14 ga Yuni, 2023 bayan ya zargi RSF da kai hari kan fararen-hula a babban birnin El Geneina na jihar Darfur ta Yamma.

Masu AlakaTRT Afrika - Fiye da mutum 1,400 sun tsere daga jihar North Darfur ta Sudan a yini ɗaya yayin da ake zafafa yaƙi

Gwamnatin Sudan ta zargi rundunar RFS da kashe shi da kuma lalata wasu sassan jikinsa, zargin da RSF ta musanta a lokacin. 

Hukumomin Sudan da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun zargi RSF da aikata munanan ayyuka masu yawa a El Geneina, ciki har da kashe ɗaruruwan mutane da kuma raba dubban al'ummar Masalit da matsugunansu.

Sudan ta tsunduma cikin yaƙi tun watan Afrilun 2023, lokacin da faɗa ya ɓarke ​​tsakanin dakarun sojin ƙasar da na RSF kan shirin haɗa rundunar dakarun RSF cikin sojin ƙasar.

Yaƙin ya haifar da ɗaya daga cikin rikicin jinƙai mafiya muni a duniya, inda ya kashe dubban mutane tare da raba miliyoyin da muhallansu.