Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka za ta karɓi ganga miliyan 30 zuwa 50 na man fetur daga Venezuela da aka sanya wa takunkumi, don a sayar da shi a farashin kasuwa.
Trump ya bayyana cewa hukumomin riƙon ƙwarya na Venezuela za su miƙa man fetur ɗin kuma shi da kansa zai kula da yadda za a gudanar da kuɗaɗen da aka sayar da shi.
"Hukumomin riƙon ƙwarya a Venezuela za su bayar da ganga miliyan 30 zuwa 50 na man fetur da aka sanya wa takunkumi ga Washington," in ji Trump.
"Man da muka samu daga Venezuela za a sayar da shi a farashin kasuwa, kuma ni ne zan kula da yadda za a gudanar da kuɗaɗen da za a samu daga sauar da shi," in ji shugaba Trump.
Trump ya ce ya umarci sakataren makamashi na Amurka da ya aiwatar da shirin nan-take.
"Na umarci sakataren makamashi da ya aiwatar da shirin nan-take," in ji shi, ya ƙara da cewa za a yi jigilar man ta amfani da tankunan ajiya sannan a aika shi zuwa tashoshin fitar da man fetur na Amurka.








