Trump ya ce Amurka za ta karɓi gangar ɗanyen mai miliyan 50 daga Venezuela
Donald Trump ya ce za su karbi ganga miliyan 30 zuwa 50 na danyen mai daga Venezuela a karkashin sabuwar yarjejeniyar da aka kulla.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka za ta karɓi ganga miliyan 30 zuwa 50 na man fetur daga Venezuela da aka sanya wa takunkumi, don a sayar da shi a farashin kasuwa.
Trump ya bayyana cewa hukumomin riƙon ƙwarya na Venezuela za su miƙa man fetur ɗin kuma shi da kansa zai kula da yadda za a gudanar da kuɗaɗen da aka sayar da shi.
"Hukumomin riƙon ƙwarya a Venezuela za su bayar da ganga miliyan 30 zuwa 50 na man fetur da aka sanya wa takunkumi ga Washington," in ji Trump.
"Man da muka samu daga Venezuela za a sayar da shi a farashin kasuwa, kuma ni ne zan kula da yadda za a gudanar da kuɗaɗen da za a samu daga sauar da shi," in ji shugaba Trump.
Trump ya ce ya umarci sakataren makamashi na Amurka da ya aiwatar da shirin nan-take.
"Na umarci sakataren makamashi da ya aiwatar da shirin nan-take," in ji shi, ya ƙara da cewa za a yi jigilar man ta amfani da tankunan ajiya sannan a aika shi zuwa tashoshin fitar da man fetur na Amurka.