‘Yansandan Nijeriya sun ƙwato kwamfuta 400, sun kama ɓarayin airtime na Naira biliyan 7.7
Waɗanda ake zargin su ne Ahmad Bala, Karibu Mohammed Shehu, Umar Habib, Obinna Ananaba, Ibrahim Shehu, da Masa'ud Sa'ad.
Jami’an ‘yansanda a Nijeriya sun kama mutane shida da ake zargi da kutse a kamfanonin sadarwa a Nijeriya da suka yi shirin satar airtime na Naira biliyan 7.7.
Wata sanarwa da Benjamin Hundeyin, kakakin rundunar ‘yansandan Nijeriya ya fitar a ranar Laraba, ta ce waɗanda ake zargin sun samu damar yin kutse cikin manyan tsarin kamfanin sadarwa ba bisa ƙa'ida ba.
Waɗanda ake zargin su ne Ahmad Bala, Karibu Mohammed Shehu, Umar Habib, Obinna Ananaba, Ibrahim Shehu, da Masa'ud Sa'ad.
Hundeyin ya ce jami'an sun ƙwace ƙananan wuraren sana’a guda biyu, shagunan sayar da kayayyaki ɗauke da kwamfutocin tafi-da-gidanka fiye da 400, wayoyin hannu 1,000, da kuma wata mota ƙirar Toyota.
Mai magana da yawun rundunar ya ce an gano wani adadi mai yawa na kuɗi a asusun bankin waɗanda ake zargin.
"Ƙungiyar 'yanta'adda ce ke da alhakin karkatar da airtime na wani kamfanin sadarwa ba bisa ƙa'ida ba, wanda ya haddasa da asarar fiye da Naira biliyan 7.7," in ji sanarwar.
"Wannan ci gaba ya biyo bayan wani ƙorafi da wani kamfanin sadarwa na Nijeriya ya shigar, wanda ya bayar da rahoton ayyukan da ake zargi da kuma waɗanda ba a ba su izini ba a cikin tsarin biyan kuɗi da ayyukan biyan kuɗi.”
Sanarwar ta ƙara da cewa bincike ya nuna cewa an yi amfani da bayanan ma'aikatan cikin gida wajen yin kutse, wanda ya bai wa masu ɓarayin damar shiga manyan tsare-tsare ba bisa ƙa'ida ba.
"Bayan makonni na shiri, an gudanar da ayyukan tsaro cikin tsari a watan Oktoban 2025 a Jihohin Kano da Katsina, tare da kama su a Babban Birnin Tarayya.
Za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken, in ji sanarwar.
"A halin yanzu, Sufeto Janar na 'Yansanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, Ph.D., NPM, ya yaba wa jami'an da ke da hannu a binciken saboda ƙwarewarsu."